Kwanturolan Hukumar Shige Da Fice na Jihar Bayelsa, James Sunday, ya bukaci sauran jami’an hukumar da su gudanar da gwaji na musamman da horo ga jami’an hukumar da ke jihohinsu kan sanin makamar aiki.
Wannan na dauke ne cikin wata sanarwa da kakakin hukumar ya fitar a ranar Talata, ta ofishin kwanturolan hukumar a jihar.
- Muna Kan Kokarin Magance Matsalar Hauhawar Farashin Kayan Masarufi —Buhari
- An Ba Ma’aikatan Bayelsa Hutun Kwana 7 Kan Ibtila’in Ambaliyar Ruwa
A cewarsa dole ne su tuna ranstuwar da suka yi lokacin fara aikin ta hanyar tsare sirri, martaba da darajar aikin, wanda kowane ma’aikacin hukumar ake sa ran zai samu horo na musamman duba da irin ayyukan da suke gudanarwa wanda ke da alaka da kasashen ketare da kuma cikin gida da kuma yin mu’amala da wadanda ba ‘yan Nijeriya ba, mutane daga kasashen waje wadanda suke sa ran samun kyakkyawar mu’amala daga gare mu ta hanyar jami’an hukumar shige da fice ta kasa ta kowace fuska.
A cewar sanarwar, ana sa ran jami’in hukumar shige da fice ya kasance mai dabi’u masu nagarta a bangarori da dama ba wai iya abin da ya shafi samar sa fasfo da sauran takardu na yin tafiye-tafiye zuwa wasu kasashe ba, alaka mai kyau da kasashen waje da kuma mu’amalar diflomasiyya, kungiyoyi da sauran hada-hada a filayen jiragen sama, tashoshin jiragen ruwa da kuma kan iyakokin kasa wanda ta nan wasu ‘yan kasashen ke kararowa zuwa Nijeriya, ana sa ran jami’i zai ba da himma wajen cika muradan aikinsa.
Horon ya zo a kan lokaci duba da samun sabbin jami’ai da ke bukatar ja a jiki, don ba su horo kulawa don ganin sun bada cikakkiyar gudunmawa, ta hanyar samun gogewa da dabi’u masu kyau ga kasa da kuma al’umma.
Kwanturolan ya ware lokaci inda ya gargadi jami’an hukumar kan amfani da kafafen sada zumunta, inda ya bukace su da su san irin abin da za su ke wallafawa a kafafen sada zumunta, wanda ya ce su guji yada abin da zai zubar da kima, daraja ko mutuncin hukumar, musamman duba da yadda zaben 2023 ke kara karatowa.
Kwanturolan ya jaddada cewae hukumar ta shirya hanyoyin daukar hukunci kan duk wani yanayi da ka iya haifar da rashin jin dadi, inda ya ce hukumar ba za ta yi kasa a gwiwa ba duk da barazanar ambaliyar ruwa da ake fuskanta a Jihar Bayelsa, amma a cewarsa hukumar ta kwashe dukkan wasu kayan aikinta da ka iya lalacewa saboda ambaliyar ruwan zuwa wani waje da babu ruwa ko raba.
Ya kara da cewar duk da jihar na cikin mawuyacin hali a dalilin ambaliyar ruwan, amma akwai wuraren da abun bai shafa ba, suna cikin yanayi mai kyau, inda ya ce hukumar ta mayar da ayyukanta zuwa rukunin gidaje da ke Okaka a cikin kwaryar birnin jihar.
Sannan ya ce ayyukan hukumar za su ci gaba da wakana a can na wucin gadi, inda ya ce hukumar a jihar da jami’anta sun yi wannan dabara ne don gudun tsayuwar ayyukanta ga jama’ar jihar.
Kwanturolan ya jaddada cewar hukumar ba ta dakatar da ayyukanta ba, “Muna yin aiki kuma jami’anmu da mutanenmu na aiki kamar kowane lokaci,” kamar yadda sanarwar ta bayyana.