Assalamu alaikum. Malam tambaya ce game da masu siyan kaya online ko kuma wanda suke kira ‘pre-order’, za a turo maka da hoton kaya ka zabi wanda kake so sai ka tura kudinka, sai a siyo, a dora riba, sannan a ba ka, saboda babu kayan a kasa lokacin da aka siyar maka, yawancin wadanda suke harkar ba su da kudin da za su mallaki kayan kafin su siyar, da kudin Kwastomomi suke siyo kayan, ya halasta ko ya haramta? Wa alaikum assalam.
A zahirin nassoshin Shari’a wannan Nau’i na cinkayya haramun ne, saboda siyar da abu ne kafin mutum ya mallake shi. Hakim Bn Hizam ya tambayi Annabi (SAW) cewa: Mutum yakan tambaye shi Hajar da ba shi da ita sai su yi ciniki ya sayar masa, sai ya je kasuwa ya sayo, sannan ya ba shi, sai Manzon Allah ya ce masa: ”
Kada ka siyar da abin da ba ka da shi” Kamar yadda Abu-dawud da Tirmizi da Nasa’i da Ibnu Majah da Imamu Ahmad suka rawaito.
Musulunci ya hana wannan Cinikayyar ne saboda akwai rashin tabbas a ciki, Idan aka samu macuci zai iya guduwa da kudin, sannan ba dole ba ne a samu kayan in an je kasuwa.
Duk cinikayyar da za ta kawo hatsaniya da sabani tsakanin musulmai haramun ce, wanda ya kiyaye dokokin Allah tabbas zai azurta shi ta inda ba ya zato, kamar yadda ya fada a suratu Addalak. Idan wakilta ki aka yi ki sayar, ya halatta ko da kayan ba sa tare dake.
Allah ne mafi sani.