• English
  • Business News
Tuesday, July 1, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Xi Jinping Da Shugaban AU Sun Taya Juna Murna

by CMG Hausa
3 years ago
in Daga Birnin Sin
0
Xi Jinping Da Shugaban AU Sun Taya Juna Murna
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Yau Jumma’a ne, shugaban kasar Sin Xi Jinping, da shugaban karba-karba na kungiyar tarayyar Afirka AU, kana shugaban kasar Senegal Macky Sall, suka aika wa juna sakon murnar cika shekaru 20 da kafa AU da kulla alakar diflomasiyya tsakanin kasar Sin da AU.

Shugaba Xi ya ce, alakar Sin da AU na dada habaka, wadda ta taka muhimmiyar rawa wajen zurfafa dankon zumunta tsakanin Sin da Afirka, da kara fadada hadin-gwiwarsu a sabon zamanin da muke ciki.

  • Ko Kasar Japan Take Son Taimakawa Afirka Cikin Sahihanci?

Ya ce yana fatan hada kai tare da Macky Sall da sauran shugabannin kasashe membobin AU, don tabbatar da aiwatar da nasarorin da aka cimma a wajen taron ministoci karo na 8 na dandalin tattaunawar hadin gwiwar Sin da Afirka wato FOCAC, da ci gaba da marawa juna baya a wasu muhimman batutuwa, da kara wakilcin kasashe masu tasowa a harkokin kasa da kasa, a kokarin bayar da gudummawa ga raya al’ummomin Sin da Afirka masu kyakkyawar makoma ta bai daya a sabon zamanin da muke ciki.

A nasa bangaren, Macky Sall ya ce, a daidai lokacin da ake cika shekaru 20 da kafa kungiyar AU, shugaba Xi Jinping ya aiko da sakon murna, al’amarin da ya shaida irin dadadden zumuncin dake tsakanin al’ummomin Afirka da Sin.

Ya sake jaddada cewa, Afirka na tsayawa haikan kan manufar kasancewar kasar Sin daya tilo a duniya, da nuna cikakken goyon-baya wajen raya al’ummomin Sin da Afirka masu kyakkyawar makoma ta bai daya. (Murtala Zhang)

Labarai Masu Nasaba

Sin Na Fatan More Fasahohi Da Kirkire-kirkire Da Kasashen Duniya Don Sa Kaimi Ga Ci Gaba Da Zamanintar Da Kasashen Duniya

Xi Ya Jaddada Bukatar Yin Aiki Tukuru Wajen Aiwatar Da Jagorancin Jam’iyya Bisa Kyawawan Akidu

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

ShareTweetSendShare
Previous Post

Wata Mata Ta Haifi ‘Ya’Ya 9 A Lokaci Daya

Next Post

Hukuncin Siyar Da Kaya Kafin Su Zo Hannu (Pre-Order)

Related

Sin Na Fatan More Fasahohi Da Kirkire-kirkire Da Kasashen Duniya Don Sa Kaimi Ga Ci Gaba Da Zamanintar Da Kasashen Duniya
Daga Birnin Sin

3 hours ago
Xi Ya Jaddada Bukatar Yin Aiki Tukuru Wajen Aiwatar Da Jagorancin Jam’iyya Bisa Kyawawan Akidu
Daga Birnin Sin

Xi Ya Jaddada Bukatar Yin Aiki Tukuru Wajen Aiwatar Da Jagorancin Jam’iyya Bisa Kyawawan Akidu

4 hours ago
Sin Ta Yi Watsi Da Bangaren Rahoton SAGO Mai Nasaba Da Binciken Tushen Cutar COVID-19
Daga Birnin Sin

Sin Ta Yi Watsi Da Bangaren Rahoton SAGO Mai Nasaba Da Binciken Tushen Cutar COVID-19

5 hours ago
Alkaluman PMI Na Sin Na Bunkasa Cikin Watanni 2 A Jere
Daga Birnin Sin

Alkaluman PMI Na Sin Na Bunkasa Cikin Watanni 2 A Jere

6 hours ago
Sin Ta Kammala Aikin Agajin Gaggawa A Yankin Da Ambaliyar Ruwa Ta Afku
Daga Birnin Sin

Sin Ta Kammala Aikin Agajin Gaggawa A Yankin Da Ambaliyar Ruwa Ta Afku

7 hours ago
Adadin Mambobin JKS Na Karuwa Yayin Da Rassanta A Matakin Farko Ke Karuwa
Daga Birnin Sin

Adadin Mambobin JKS Na Karuwa Yayin Da Rassanta A Matakin Farko Ke Karuwa

8 hours ago
Next Post
Hukuncin Siyar Da Kaya Kafin Su Zo Hannu (Pre-Order)

Hukuncin Siyar Da Kaya Kafin Su Zo Hannu (Pre-Order)

LABARAI MASU NASABA

Sin Na Fatan More Fasahohi Da Kirkire-kirkire Da Kasashen Duniya Don Sa Kaimi Ga Ci Gaba Da Zamanintar Da Kasashen Duniya

Sin Na Fatan More Fasahohi Da Kirkire-kirkire Da Kasashen Duniya Don Sa Kaimi Ga Ci Gaba Da Zamanintar Da Kasashen Duniya

June 30, 2025
Jarumin Matashi Ya Ragargaji  Wani Ɗan Fashi A Kano

Jarumin Matashi Ya Ragargaji  Wani Ɗan Fashi A Kano

June 30, 2025
Xi Ya Jaddada Bukatar Yin Aiki Tukuru Wajen Aiwatar Da Jagorancin Jam’iyya Bisa Kyawawan Akidu

Xi Ya Jaddada Bukatar Yin Aiki Tukuru Wajen Aiwatar Da Jagorancin Jam’iyya Bisa Kyawawan Akidu

June 30, 2025
Sin Ta Yi Watsi Da Bangaren Rahoton SAGO Mai Nasaba Da Binciken Tushen Cutar COVID-19

Sin Ta Yi Watsi Da Bangaren Rahoton SAGO Mai Nasaba Da Binciken Tushen Cutar COVID-19

June 30, 2025
Bello Turji, Yana Neman Ayi Sulhu Bayan An Kashe Yaronsa

Tawagar Gwamnatin Tarayya Ta Miƙa Saƙon Ta’aziyyar Shugaba Tinubu A Gidan Ɗantata Na Madina

Tawagar Gwamnatin Tarayya Ta Miƙa Saƙon Ta’aziyyar Shugaba Tinubu A Gidan Ɗantata Na Madina

June 30, 2025
Alkaluman PMI Na Sin Na Bunkasa Cikin Watanni 2 A Jere

Alkaluman PMI Na Sin Na Bunkasa Cikin Watanni 2 A Jere

June 30, 2025
CAF Za Ta Ƙaddamar Da Sabon Kofin Gasar Ƙasashen Afrika Na Mata

CAF Za Ta Ƙaddamar Da Sabon Kofin Gasar Ƙasashen Afrika Na Mata

June 30, 2025
Sin Ta Kammala Aikin Agajin Gaggawa A Yankin Da Ambaliyar Ruwa Ta Afku

Sin Ta Kammala Aikin Agajin Gaggawa A Yankin Da Ambaliyar Ruwa Ta Afku

June 30, 2025
Matasa Sun Ƙona Ofishin NDLEA, Sun Kutsa Fadar Sarki A Kwara

Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci