Daga Bashir Isah
Alal hakika, al’ummar Jihar Binuwai ba za su taba mancewa da daminar 2017 ba sakamakon irin ibtila’in ammbaliyar ruwa da ya auku gare su albarkacin daminar, lamarin da ya yi sanadiyyar hasarar rayuka da dimbin dukiyoyi kama daga amfanin gona zuwa gidaje da sauransu masu yawan gaske, wanda hakan ya raba dimbin jama’ar da lamarin ya shafa da muhallansu inda suka koma rayuwa a sansanoni.
Ko shakka babu, ibtila’in ambaliyar da Jihar Binuwai ta fuskanta, akwai yiwuwar damuwar hakan ba za ta takaita ga jama’ar jihar kadai ba, mai yiwuwa lamarin zai haifar da karacin abinci a jihar da ma kasa baki daya. Bayan wannan, lamarin ka iya zama sanadiyyar dullar wata cuta da dai sauransu. Masana na ra’ayin cewa, ambaliyar ta auku ne sakamakon mamakon ruwan sama da aka samu jihar.
Bisa la’akari da abin da ya auku, wannan ya sa a kwanakin baya aka ji gwamnan jihar Samuel Ortom na gargadin cewa, duba da irin matsalar ambaliyar ruwa da ta shafi Jihar Binuwai, akwai yiwuwar nan gaba a wannan shekara, jihar da ma kasa baki daya a yi fama da matsalar karancin abinci kasancewar Jihar Binuwai na daya daga jihohin da ke kan gaba wajen samar da abincin da al’ummar kasar nan ke ci, sai kuma ga shi ambaliya ta yi gaba da amfanin gona masu yawan gaske da aka noma. Gwamnan ya yi wadannan kalamai ne a lokacin da ya kai ziyarar gani-da-ido a wuraren da lamarin ya shafa, inda ya nuna damuwarsa ganin dimbin gonaki da ambaliyar ta kwashe hada da wasu amfanin gona da aka rigaya aka girbe duk a tsakanin mako guda kacal.
Domin tabbatar da duka wadanda lamarin ya shafa sun samu kulawar da ta dace, Gwamna Ortom ya ce an bude sansani guda biyu a Makurdi babban birnin jihar tare da umurtar shugabannin kananan hukumomi 23 da jihar ke da su a kan su yi amfani da wasu gine-ginen makarantun firamare a yankunansu domin bai wa jama’ar da ambaliyar ta shafa mafaka.
Gwamna Ortom bai yi kasa a gwiwa ba wajen mika godiyarsa ga Shugaba Muhammadu Buhari dangane da tallafi na wasu kayayyakin amfani da ya bai wa wadanda lamarin ya shafa ta hannun Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta Kasa ko kuma NEMA a takaice.
Kamar yada rahotanni suka nuna, a dalilin wannan mummunar ambaliya, an yi hasarar rayuka da gonaki da gidaje masu yawa, hada da gadajoji da hanyoyi wanda hakan zai haifar da tsaiko a zirga-zirgar mutanen yankunan na wani tsawon lokaci. Daruruwan mutane ne suka rasa matsuguninsu a wannan ibtila’in.
Rahotanni daga jihar sun tabbatar da cewa, lamarin ya fi tsanani ne a wasu kauyuka guda goma sha biyu ciki har da; kauyen Tse-Adorogo inda gwamnan jihar ya fito, da Tse-Igba da Tse-Akor da Tse-Terzar da Tse-Abi da Tor Kpande da dai sauransu.
Sabuwar hanyar nan ta Daudu zuwa Gbajimba da Jami’ar Harkokin Noma da ke Makurdi, duk ambaliyar ta shafe su. Idan dai za a iya tunawa, ko a shekarar 2012 Jihar Binuwai ta fuskanci ibtila’in ambaliya inda aka yi hasarar rayuka da dukiyoyi da dama.
Domin gane wa idanunta irin ta’asar da ambaliyar ta yi a Jihar Binuwai, ya sanya Gwamnatin Tarayya a karkashin jagorancin mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ta kai ziyara ta musamman a jihar, inda a tashin farko mataimakin shugaban kasar ya ziyarci sarkin Tibi Ocibirigh James Ayatse, kafin daga bisani ya karasa wasu daga cikin wuraren da ambaliyar ta shafa. Yayin ziyarar tasa ga sarkin Tibi, Osinbajo ya yaba da irin karbar da ya samu a fadar sarkin.
A hannu guda sa’ilin da yake magna da gwamnan jihar Samuel Ortom, Osibanjo ya bayyana cewa kafin wannan lokaci, ya so kawo ziyara a jihar a lokuta da dama amma hakan bai yiwu ba sai a wannan karo. Ya ce: “Na zo muku da gaisuwa daga Shugaba Muhammadu Buhari wanda ya nuna damuwarsa matuka a kan ambaliyar da ta same ku wanda hakan ne ma ya sanya shugaban ganin dacewa in zo da kaina tare da wasu muhimman ministoci da hukumomi da zummar samar da mafita ta din-din ga matsalar ambaliya a wannan jiha”.
A cewar Osinbajo, “Idan aka dubi wannan batu da kyau, za a ga cewa matsalar nan ta ambaliya ba yau ne farau ba, kuma haka za ta ci gaba da aukuwa muddin ba a dauki matakin dakile ta ba baki daya. Don haka wannan ziyara tana da muhimmanci matuka, domin kuwa bayan kammala ta, za mu zauna mu tattauna tare da Shugaban Kasa da gwamnan Binuwai har ma da Tor Tib a kan yadda za a samar da mafita ga wannan matsalar da ta ki ci, ta ki cinyewa”.
“Sai dai wani abin takaicin shi ne, ba mu ga wani yunkurin kirki da aka yi ba don ganin an dakile wannan kalubalen, saboda kudaden da aka ware don cimma bukatar hakan sun yi batan dabo musamman ma a gwamnatin da ta gabata. Ina ganin duk matakin da aka yanke za a dauka, tilas mu tabbatar da cewa kudaden da aka ware domin yin aikin an sarrafa su ta hanyar da ta dace ta yadda a karshe a samu kwalliya ta biya kudin sabulu”.
“Kuma ina kyautata zaton gwamnan jihar, alamu sun nuna a shirye yake ya yi abin da ya kamata, a ganina Jihar Binuwai ta yi dace da shugabancin da zai samar da irin cigaban da ake bukata”, in ji Osibanjo.
A karshe, Osinbajo ya jaddada bukatar da ke akwai na tilas a yi hakuri saboda aikin ba abu ba ne da zai yiwu a cikin dare daya, “Ya zama tilas a yi hakuri tare da bai wa gwamnati da hukumomi hadin kan da suke bukata don hakarmu ta cimma ruwa a karshen lamari”.
Tun bayan aukuwar ibtila’in, shugabanni da hukumomi da kungiyoyo hada da daidaikun jama’a, an yi ta jajanta wa Jihar Binuwai da ma al’ummarta, daga ciki har da shugaban Majalisar Wakilai Honarabul Yakubu Dogara wanda a wani bayani da ya fito daga ofishinsa, an ji shi yana cewa Majalisar Wakilai ta kai matakin karshe na neman samar da ingantaccen tsarin da zai hana aukuwar irin wannan ambaliyar a gaba.
A jawabin nasa ya ce, “Ina jajanta wa gwamnatin Jihar Binuwai da jama’arta dangane da hasara daban-daban da aka samu sakamakon ambaliyar da ta auku a jihar wadda ta yi sanadiyyar raba mutane sama da dubu dari da matsuguninsu. Hakika, lamarin ya munana da har ya ja hankalin da dama a kan bukatar da ke akwai na a hanzarta daukar matakin kare muhallanmu”. Ya ci gaba da cewa, Majalisar Wakilai ta yi nisa wajen nazarin samar da dokar da za ta bada damar kafa hukuma ta musamman da za ta rika kula da batutuwan da suka shafi sauyin yanayi. Daga nan sai ya yi kira ga Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta Kasa da danginta da su hanzarta kai wa wadanda ambaliyar ta shafa a Jihar Binuwai dauki”.
Sai dai wasu ‘yan jihar na ra’ayin cewa, da a ce dan kwangilan da aka bai wa aikin daidaita matsalar zaizayar kasa tun a shekarar 2000 ya kammala aikinsa, ko shakka babu da an samu zarafin dakile matsalar ambaliya a birnin Makurdi da dadewa. Kwangilar da aka kiyasta ta kai sama da naira bilyan biyu, an bada aikinta ne tun a tsohuwar gwamnatin George Akume, inda aka bukaci a samar da wadatacciyar hanyar ruwa daga Wurukm zuwa Achusa ya zuwa Wadata.
Bayan ra’ayoyi mabambanta da aka samu dangane da karfin barnar da ambaliyar ta yi, daga bisani Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta Jihar ko kuma SEMA a takaice, ta sanar a rahotonta da fitar cewa kimanin mutane dubu dari da goma ne kuma a tsakanin kauyuka ashirin da hudu hada da babban birnin jihar Makurdi suka rasa matsuguninsu a dalilin ambaliyar.
A cewar sakataren hukumar Mista Boniface Ortese, “Wuraren da lamarin ya shafa sun hada da: Achusa, Idye, Kasuwar Wurukum, Genabe, Demekpe, Kasuwar Wadata, Katungu, Agboughul-Wadata da dai sauransu. Ta bakinsa, “A yankin Achusa, kimanin gidaje 200 ne ambaliyar ta shafa inda mutum 5,125 suka rasa matsuguninsu. Sai kuma bayan Cibil Serbice Commission, inda a nan ma wasu gidaje 200 ba su tsira ba lamarin da ya yi sanadiyyar raba mutane 5,777 da muhallansu”.
“A yankin Genabe, gidaje guda 200 lamarin ya shafa tare da raba mutum 5,021 da mazauninsu. Haka dai lamarin yake a yankin Kasuwar Wurukum, inda mutum 1000 ne suka rasa matsuguninsu bayan da ambaliyar ta lalata gidaje har guda 218. Sai kuma yankin Kasuwar Wadata, inda ambaliyar ta tashi gidaje 150 tare da raba mutane kimanin su 4,300 da mazaunisu”.
Jami’in ya ci gaba da cewa, “A yankin Industrial Layout, mutum 4,310 suka rasa wurin zamansu bayan da ambaliyar ta ci gidaje 69, sai kuma mutane 6,031 da suka rasa mazauninsu sakamakon gidaje 137 da ambaliyar ta shafa a yankin Katungu, yayin da a yankin Agboughul-Wadata, gidaje 201 ne ruwan ya lalata tare da raba mutane 5,728 mutsuguninsu”, in ji Ortese.
Bugu-da-kari, sakataren ya ce tuni aka samar da sansani a babbar kasuwar nan ta kasa-da-kasa a jihar domin taimaka wa wadanda lamarin ambaliyar ya shafa. Tare da cewa, tun bayan kafa sansanin an samu tallafin kayayyakin amfani gwargwado daga sassa daban-daban.
Sai dai kuma, ana dar-dar game da yiwuwar bullar wata cuta musamman ma a yankunan da ambaliyar ta shafa. Domin kuwa, bayanan Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta Jihar sun tabbatar da mutuwar mutum uku yayin da rayuwar mutum 110, 000 da suka tsira da rayukansu ke cikin hadari kamuwa da cututtuka.
A nasa bangaren, Shugaba Buhari ya shiga sahun masu jajanta wa Gwamnatin Jihar Binuwai da al’umarta game da ibtila’in ambaliya da ya same su. Shugaban ya yi Magana ne ta bakin kakakinsa Malam Garba Shehu, inda ya ce, “Shugaba Buhari ya samu labarin aukuwar ambaliyar ruwa a Jihar Binuwai, lamarin da ya raba dubban mutane da matsuguninsu a tsakanin kananan hukumomi goma sha biyu a fadin jihar. Tare da cewa, shugaban ya bada umarnin a hanzarta kai tallafin da ya dace domin amfanin jama’ar da lamarin ya shafa”.
Kawo yanzu dai Gwamnatin Tarayya ta yi alkawarin yashe Kogin Binuwai tare da samar da wani sabon tsari da zai taimaka wajen aikin yashe kokin domin dakile matsalar ambaliya a jihar baki daya.