- Sai Da Suka Shafe Minti 30 A Binne Kafin Kawo Musu Dauki
- Halin Da Muka Tsinci Kanmu A Ciki – Malamin Almajiran
- Jama’a Na Ci Gaba Da Tururuwar Shaida Lamarin
- Tambayoyin Da Mutane Ke Yi Ga Gwamnatin Kebbi
Al’ummar Jihar Kebbi har ma da sauran sassan Nijeriya sun shiga alhini bayan rasuwar wasu almajirai takwas sakamakon wani dutse da ya yanke ya fado kan almajiran na Makarantar Allon Malam Dan Umma da ke Unguwar Badariya, cikin Karamar Hukumar Birnin Kebbi.
A safiyar ranar Asabar 20 ga watan Afrilun 2024, da misalin karfe 8 na safe ne iftila’in ya auku. Masana sun bayyana cewa tarihi ya nuna akalla dutsen ya kai kimanin shekaru 80 zuwa 100 da fitowa inda yake ta girma har ya mamaye waje mai yawan gaske.
- Gwamnan Jihar Kebbi Ya Amince Da Fitar Da Miliyan 309.5 Don Tallafawa Ɗaliban Da Ke Karatu a Ƙasashen waje
- Jami’an Tsaro sun Ceto Mata Biyu da aka Yi Garkuwa da Su A Kebbi
Haka kuma sun kara da cewa a lokacin da ba a fara amfani da kasar siminti ba sosai a yankin, jama’a da dama suna amfani da burbushin dutsen ne da kasar da yake cakude da shi wajen gina gidaje. Daga baya kuma dutsen ya koma filayen jama’a har ma da yawa sun gina gidajen kwana ta yadda a halin yanzu gidaje ne a ko ina a yankin da hatsarin ya auku.
Saboda wannan al’ada ta amfani da kasar dutsen ne, almajiran da suka je hako kasa bisa umarnin malaminsu domin su gyara wasu ramuka da ke dakunansu, suna kan aiki kwatsam dutsen ya yanke ya taushe akalla su 10, inda nan take takwas suka riga mu gidan gaskiya, biyu suka tsira tare da garzayawa da su asibitin tunawa da Sarki Yahaya. Sai dai daga baya daya shi ma ya rasu, zuwa lokacin hada wannan rahoto almajiri daya ne ke jinya.
Rahotanni sun nunar da cewa wadanda hatsarin ya rutsa da su sun kai kimanin minti 30 a binne kafin a kawo musu agajin gaggawa daga jama’ar da ke unguwar.
Almajiran da suka rasa rayukansu a nan take da suka hada da Muhammad Bawada, Musa Kambaza, Dan Sayyada Kambaza, Nasiru Cheberu, dukkansu sun fito ne daga Karamar Hukumar Gwandu, sai kuma Yakubu da Aminu da sauransu da suka fito daga wurare daban-daban. Dukkan almajiran da suka rasa rayukansu babu wanda ya kai shekara 20 da haihuwa.
Binciken wakilinmu ya gano cewa wannan shi ne hatsari na farkon a tahirin fitowar dutsen duk da cewa mafi yawan gidajen jama’ar Unguwar Badariya da kewaye duk da kasar dutsen ne aka gina su amma ba a sumu irin wannan ba sai a kan wadannan almajiran.
Da yake tsokaci kan lamarin, malamin almajiran, Malam Dan Umma ya tabbatar da mutuwar almajiran takwas nan take, kana ya kara da cewa, “Yau daya ce daga cikin ranaku mafi bakin ciki a rayuwata. Abin da ya faru shi ne, na ba su umarnin cewa su je su gino kasar don gyara ramukan da ke cikin dakunansu saboda ruwan damina na zuwa. Daga nan sai suka tafi bakin dutsen da ke kusa da makarantar.
“Bayan mintoti kafin dawowarsu, sai wasu daga cikin almajiran suka sheko da gudu suna wayyo, wayyo, dutse ya taushe almajirai da suke ginar kasar a cikin dutsen. A nan take na garzaya wurin da lamarin ya faru, inda na tabbatar da mutuwarsu yayin da biyu da suka tsira kuma aka garzaya da su asibiti don tabbatarwa ko akasin hakan.”
Malam Dan Umma ya ci gaba da cewa, an ajiye gawarwakin almajiran da suka rasu a dakin ajiyar gawa na asibitin tunawa da Sarki Yahaya da ke Birnin Kebbi, kafin a kai su gidajen iyayensu domin yi musu jana’iza.
Bayan faruwar lamarin jama’ar unguwar Badariya da ma na cikin garin Birnin Kebbina ci gaba da tattaki zuwa bakin dutsen don gane wa idanunsu irin yadda lamarin ya faru.
Wasu da suka zanta da wakilinmu, sun bayyana ra’ayin cewa bai kamata a ce malamin almajiran ya ba su umarnin su je su hako kasar gyaran dakunansu ba, saboda kananan yara ne kuma wajen da suke kwana mallakin malamin don haka shi ya kamata ya gyara ba almajiran ba.
Sun kara da fadin cewa idan damina ta kankama, ruwa na gaggarowa daga dutsen zuwa cikin gidajen mutane saboda wasu gidajen a bisa hanyar ruwan daminar aka gina su. Ta hakan ne ake yawan samun matsalolin ambaliya da ke lakume rayukkan jama’a da kuma rasa matsuguni wanda sai sun nemi agajin gaggawa daga gwamnati da kuma wasu hukumomi masu ba da agajin gaggawa idan aka samu ambaliyar ruwan sama.
Wakazalika, abin da mutane ke kara tambaya a kai shi ne, mutanen da ke zama kusa da dutsen sun samu izinin haka kuwa sannan hukumar kula da filaye da ta bunkasa birane sun yi la’akari da irin hadurran da ke tattare da zama a wannan wurin kuwa?
A halin yanzu dai jama’a sun zura ido su ga wane irin mataki ne Gwamnatin Jihar Kebbi za ta dauka domin riga-kafin lamarin a gaba.