Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta ICPC ta fara bin diddigin ayyukan mazabu na naira biliyan 21 a fadin Jihar Kaduna.
Hukumar ta ce matakin na daga cikin kokarinta na tabbatar da gaskiya da rikon amana wajen gudanar da ayyuka ga jama’a.
- An Gano Buhunan Shinkafar Tallafi 16,800 Mai Nauyin Kilo 50 Da Aka Sauyawa Buhu A Kano
- Yara 160,000 Ke Rayuwa Da Cutar Ƙanjamau A Nijeriya —NACA
Da yake zantawa da manema labarai a Kaduna, babban sufeto na ICPC, Haruna Aminu, wanda ya wakilci sashen bin diddigi na mazaba da zartarwa a karkashin jagorancin shugaban ICPC, Dakta Musa Adamu Aliyu, ya ce hukumar na bibiyar ayyuka 60 a fadin Jihar Kaduna.
“Mun zo nan ne domin bin diddigin ayyuka kusan 60 a fadin Jihar Kaduna da adadin kudinsu ya kai naira biliyan 21. Mun fara ne a ranar Laraba a yankin Kafanchan, inda muka binciki akalla ayyuka 21. Yanzu haka muna babban garin Kaduna, Unguwar Kabala, muna mai da hankali kan ayyuka irin su fitulun titi mai amfani da hasken rana da aka saka a fadin garin.
“Gaba daya dai, a kan aikin hasken rana, mun ga matakin da ake kai na aiwatarwa, sannan kuma daga dayan kusurwar, mun sami damar gano wasu ayyukan. Wannan aiki ne da ya taba rayuwar mutane,” in ji shi.
Ya kuma ce hukumar za ta ga yadda za ta tura dan kwangilar ya kammala aikin, inda ya nuna cewa babu wani dan kwangila da za a tsallake saboda ba zai yiwu ba su karbi kudin gwamnati su tafi ba tare da kammala ayyuka ba.
Ya ce zamanin watsi da ayyuka ya wuce domin an ba su dukkan umarni da goyon baya don tunkarar duk wadanda suka kasa kamala ayyukansu a kan lokaci.
Aminu ya bayyana cewa jinkirin da aka samu wajen kammala wasu ayyuka, musamman fitilun titi masu amfani da hasken rana ya kawo cikas ga tasirinsa ga al’umma.
“Wadannan ayyuka na da muhimmanci wajen inganta rayuwa a Jihar Kaduna. Idan aka kammala a shekarar da ta gabata kamar yadda aka tsara, da a yanzu za su kawo gagarumin sauyi,” in ji shi.
Ya ce mataki na gaba na wannan yunkuri zai kunshi dakushe ‘yan kwangilar da suka kasa gudanar da ayyukansu, da tabbatar da cewa ‘yan kasa sun samu ribar dimokuradiyya.