IGP Adamu Zai Garzaya Kotu Bisa Zargin Bada Rashawa Don Tsawaita Wa’adinsa

Biafara

Daga Rabiu Ali Indabawa,

Rundunar ‘yan sanda ta kasa ta karyata rahoton da wata kafar yada labarai ta yada a kan IGP Adamu, babban Sufeto Janar na rundunar ‘yan sanda. Jaridar SaharaReporters ta wallafa cewa IGP Adamu ya bayar da cin hancin Naira biliyan 2 domin a kara masa wa’adi.

Kakakin rundunar ‘yan sanda, Frank Mba, shi ya karyata rahoton tare da sanar da cewa IGP Adamu zai nemi hakkinsa a kotu. “Mohammed Adamu, Sufeto Janar na rundunar ‘yan sanda (IGP), bai biya Naira biliyan 2 domin a tsawaita wa’adin mukaminsa na IGP ba”, a cewar mai magana da yawun rundunar yan sanda na kasa, Frank Mba.

Mba ya bayyana cewa shugaban kasa ne kawai ya ke da alhakin kara wa’adin mukamin IGP, kuma shi din ne ya ga dama ya kara ba wai cin hanci ne aka bayar ba, kamar yadda TheCable ta rawaito.

A ranar Litinin ne wa’adin Adamu ya ke karewa tare da yin ritaya daga aiki bayan da ya shafe shekaru 35 yana aikin gwamnati, wannan dai wata doka ce daga cikin kundin mulkin kasar Nijeriya na yin ritaya bayan wa’adin aikin shekaru 35.

Sai dai, IGP Adamu ya damu sahalewar shugaban kasa Muhammadu Buhari na ya ci gaba da aiki na tsawon watanni uku nan gaba, inda kuma daga bisani ne rahotanni suka ci gaba da yawo a kafofin sada zumunta na cewar Adamu ya biya cin hanci ne domin a kara wa’adin mukaminsa.

“Batun cewa wai IGP bai yi bikin kara wa’adin mukamin na sa ba, wannan wani al’amari ne na dama, amma dai muhimmancin kara wa’adin ya rataya ne kan aiki tukuru domin sauke nauyin da ya rataya a wuyansa.”

Sifeto Janar na rundunar ya ce rundunar ‘yan sanda a karkashin shugabancinsa ta jajirce wajen inganta tsaron dukiya da rayukan al’umma.

Exit mobile version