ILIMI A KANO: ’Ya’yan Talakawa Ne Kadai Ke Zuwa Makarantun Gwamnati A Jihar Kano

Daga Nasiru Salisu Zango

Halin da ilimi ke ciki a Kano abin takaici ne matuka kuma tashin hankalin shine har yanzu ba a dauki hanyar yiwa tufkar hanci ba.na shiga jimami lokacin da naga wata daliba wacce ta kammala primary zata tafi sakandare amma baza ta iya hada jimla daya ba,amma duk da haka taci jarrabawar tafiya sakandaren. Nasan kuma zaku iya gwadawa kuje makarantar gwamnati dake kusa daku domin gwada matsayin karatun daliban, tabbas zaku sha mamaki. Shin laifin waye? Gwamnati ce? Malamai ne ko iyaye? Na san dai ba haka ake a makarantun kudi ba.

Wannan matsalar ta dade sosai amma kowa yayi shiru, ba tare da la’akari da gararin da ka iya faruwa ba, abin ya zama galibi mutane a Kano sun yanke kauna da makarantun gwamnati, wannan ya sa tun daga kan gwamna zuwa kwamishinan ilimi da manyan kusoshin gwamnati da darektocin ilimi da duk wani mai hali, “yayansu suna makarantun kudi. Watakila wannan ne ma yasa akayi shakulatun bangaro da irin wadannan makarantu, domin da ace ‘ya’yansu a makarantun gwamnati suke, wallahi ko ta halin kaka sai an gyara. Wannan ra’ayina kenan.

Su kuma makarantun kudi sun auna sun fahimci cewar duk mai hali dole sai yazo gare su,dan haka suke tatsar mutane yadda ransu ke so,ita kuma hukumar lura da makarantu masu zaman kansu tayi shiru bata yunkurin kare jama’a burin su kawai abin da zasu samu,dan haka ne ma zarge zargen cin hanci da rashawa yayi katutu a wannan hukuma. Zancen da nake muku yawanci makarantun kudi duk shekara sai sun kara kudi, domin sun san mutane basu da zabi. Babban abin takaicin dake bani mamaki shine yadda galiban makarantun kudi a Kano suke cin karansu ba babbaka, su tilastawa iyaye sayen litattafai a hannu su, su kirkiro kayan makaranta (uniform) wanda zai wahalar samu kuma su yanka kudi san ransu dole iyaye su saya.

Wani abin takaici shine yadda wasu makarantun ke cewar daga kasar waje suke yo odar yadin hakan ne yasa shi yin tsada, ban da Nijeriya ina ake haka? Gaskiya ya kamata a yi wa tufkar hanci tun da sauran lokaci. Ina kira ga hukumar lura da makarantu masu zaman kansu a Kano da hana makarantun sayar da uniform da littafai, sannan ayi irin na gwamnatin baya wato a tabbatar an sa ido akan su domin hana karin kudi barkatai. Sannan kuma ya kamata ayi nazari akan halin da makarantun gwamnati ke ciki domin abin takaici ne.

Exit mobile version