ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Illar Shan Taba Sigari Da Dangoginta

by Sani Anwar
3 weeks ago
Sigari

Shan taba sigari da dangoginta, waɗanda suka haɗa da irin su tabar wiwi, shisha, ɓape da sauran makamantansu, na da matuƙar illa ga lafiyar Ɗan’adam.

Duk da cewa, ba lallai ba ne su ƙunshi sinadarai iri ɗaya ba, amma amfani da waɗannan abubuwa na da matuƙar illa ga lafiyar masu shan su, ko sun sani ko ba su sani ba. Ga dai wasu daga cikin manyan illolin shaye-shayen kamar haka:

1- Lalata huhu: Shan tabar sigari ko wiwi da sauran dangoginsu, na lalata huhu ƙwarai da gaske, suna rage ƙarfin numfashi, sannan kuma suna ƙara haɗarin cututtukan numfashi da kuma haifar da kansar huhu.

ADVERTISEMENT

2- Suna lalata zuciya da jijiyoyin jini: Wannan shaye-shaye, yana ƙara haɗarin ciwon zuciya da bugun jini da kuma matsalolin jijiyoyin jini, ba tare da mutum ya farga ba. shi ya say a zama wajibi a kiyaye ƙwarai da gaske

3- Lalata baki da haƙora: Shaye-shayen tabar wiwi da sauran dangoginta, na iya jawo warin baki da cututtukan dasashi da kuma lalacewar haƙora da kansar baki baki-ɗaya.

LABARAI MASU NASABA

An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

4- Kamuwa da cutar kansa: Wasu sinadarai da ke cikin hayaƙi, na iya lalata ƙwayoyin jiki, sannan kuma su ƙara haɗarin kansar sassan jiki daban-daban.

5- Matsalar ƙwaƙwalwa: Sinadaran da ke cikinsu, na iya sanya wa mutum ya saba da su sosai, har ya yi wahalar dainawa (addiction), ta inda ko da wani ya yi yunƙurin dainawa, sai rashin lafiya ta kama shi, ya ji babu abin da yake yi masa daɗi, har sai ya koma ya ci gaba da shaye-shayen.

6- Tsarin haihuwa: Amfani da su na iya shafar lafiyar tsarin haihuwa ko ga mace ko namiji. A lokacin ciki kuma, shan su na ƙara haɗarin kamuwa da wasu matsaloli ga uwa da kuma shi kansa jaririn da yake ciki.

7- Hayaƙn da wasu ke shaƙa: Wanda ba ya sha ma na iya cutuwa, musamman idan yana yawan shaƙar hayaƙin tabar da wani ke sha, musamman ma ga yara ƙanana.

A taƙaice dai, cutarwar taba da dangoginta, ba su tsaya a kan iya huhu kawai ba, suna iya shafar kusan dukkanin sassan jikin Ɗan’adam baki-ɗaya.

Daina amfani da su kuma kwata-kwata, yana rage haɗarin cututtuka da dama, sannan kuma yana taimaka wa jiki ya fara murmurewa cikin ɗan wani lokaci.

Saboda haka, ya kamata a kiyaye, a kuma yi hattara sosai da sosai, domin kuwa, lafiya iya ce uwar jiki, babu mai fushi ita.

Sigari
Sani Anwar
+ postsBio
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    Ko Kun San Amfanin Kwanciya Da Bangaren Hagu?
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    2027:Mata Shida Da Ke Takarar Neman Shugabancin Nijeriya
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    Dambarwa A Kasuwancin Iyalan Indimi
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    Abubuwan Da Ba A Faɗa Ba Game Da Auren Gata Da Gwamnatin Jihar Kano Ta Jagoranta

MASU ALAKA

An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu
Labarai

An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

September 9, 2026
Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu
Manyan Labarai

Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

September 9, 2026
’Yansanda Sun Cafke Matar Da Ta Kwara Wa Maƙociyarta Tafasasshen Ruwan Zafi A Abuja
Manyan Labarai

’Yansanda Sun Cafke Matar Da Ta Kwara Wa Maƙociyarta Tafasasshen Ruwan Zafi A Abuja

September 9, 2026
Next Post
Mataimakiyar Babban Magatakardar MDD Ta Jinjinawa Manufofin Kasar Sin Na Shawo Kan Kwararar Hamada

Mataimakiyar Babban Magatakardar MDD Ta Jinjinawa Manufofin Kasar Sin Na Shawo Kan Kwararar Hamada

LABARAI MASU NASABA

Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

September 9, 2026
An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

September 9, 2026
Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba

Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba

September 9, 2026
Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa

Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa

September 9, 2026
Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

September 9, 2026
Renon Matasa A Kan Kyakkyawar Turba Ginshiki Ne Na Gina KasaBy

Renon Matasa A Kan Kyakkyawar Turba Ginshiki Ne Na Gina KasaBy

September 9, 2026
Bikin CIFTIS Zai Ingiza Bude Kofa A Kasar Sin

Bikin CIFTIS Zai Ingiza Bude Kofa A Kasar Sin

September 9, 2026
“Ajin Tashar Sararin Samaniya Na Hong Kong Da Macau” Ya Kara Wa Matasa Sha’awar Kimiyya Da Karfafa Kishin Kasa

“Ajin Tashar Sararin Samaniya Na Hong Kong Da Macau” Ya Kara Wa Matasa Sha’awar Kimiyya Da Karfafa Kishin Kasa

September 9, 2026
’Yansanda Sun Cafke Matar Da Ta Kwara Wa Maƙociyarta Tafasasshen Ruwan Zafi A Abuja

’Yansanda Sun Cafke Matar Da Ta Kwara Wa Maƙociyarta Tafasasshen Ruwan Zafi A Abuja

September 9, 2026
Taron Kolin Urumqi Ya Mayar Da Hankali Kan Kwarewar Shugabanci A Xinjiang Da Muhimmancinta Ga Duniya

Taron Kolin Urumqi Ya Mayar Da Hankali Kan Kwarewar Shugabanci A Xinjiang Da Muhimmancinta Ga Duniya

September 9, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.