Mataimakiyar babban magatakardar MDD, kuma babbar sakatariyar yarjejeniyar yaki da kwararar hamada ta majalisar ko UNCCD, Yasmine Fouad, ta jinjinawa manufofin kasar Sin na kandangarki da shawo kan kwararar hamada.
Fouad, wadda ta yi tsokacin a baya-bayan nan, yayin zantawa da wakilin kafar CMG ta kasar Sin, ta ce nasarar da Sin din ta cimma a wannan fage, na da nasaba da karfafan manufofinta na siyasa da tsari na dogon lokaci.
Ta ce, a hamadar Taklamakan, wadda ita ce hamada mafi girma a kasar Sin, kana ta biyu mafi girma dake fadada a duniya, an gina shingen itatuwa don dakile bazuwar hamadar, ta yadda shingen na tsirrai ya kewaye kilomita 3,046, tamkar wani koren-mayafi da ke dakile, da kuma shawo kan matsawar rairayin hamadar, yayin da a daya bangaren kuma yanayin muhallin halittun yankin ke ci gaba da inganta.
Dangane da hakan, Fouad ta ce, duk wani mataki na jagoranci da Sin ke aiwatarwa, na gudana daidai wa daida da kuma karko, yayin da kasar ke kara fadada buri na cimma nasarar kammala wannan koren-mayafi. A cewar jami’ar, Sin na iya yin hadin gwiwa tare da karin kasashe a sassa masu nasaba.
Ga misali, a nahiyar Afirka, Sin da kasashen nahiyar sun kuduri aniyar yin hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare, don gina “Babbar Ganuwar Itatuwa”. Kuma kamata ya yi a gaggauta hakan, tare da shigar da karin kwarewar Sin, da fasahohi, da nasarori na hakika don cimma nasarar da aka sanya gaba. (Saminu Alhassan)













