ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, September 10, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ko Kun San Amfanin Kwanciya Da Bangaren Hagu?

by Sani Anwar
2 weeks ago
Kwanciya

Yanayin yadda muke barci, na taka muhimmiyar rawa kwarai da gaske ga lafiyarmu. Haka zalika, bincike ya nuna cewa, barci a gefen hagu; na taimaka wa lafiyar jiki kwarai da gaske.

Bari mu bincika dalilai guda takwas, wadanda suka sa wannan yanayi na barci a bangaren hagu zai kasance mai fa’ida ko taimaka wa lafiyar jikin Dan’adam.

1-Abinci na saurin narkewa: Kwanciya da barin hagu na taimakawa wajen saurin narkewar abinci daga kananan hanji zuwa manyan hanji cikin sauki. Sannan, yana taimaka wa dabi’ar tsarin jiki ta yadda zai yi aiki yadda ya kamata tare kuma da hana kumburi da rashin jin dadi bayan cin abinci.

ADVERTISEMENT

2-Yana rage ciwon zuciya: Ga masu fama da kwannafi ko zafin kirji, kwanciya da bangaren hagu na taimaka masu wajen rage zafin ko hana kwannafi baki-daya, tare da ba su damar yin barci mai dadi.

3-Taimaka wa lafiyar zuciya: Kwanciya da bangaren hagu na taimaka wa lafiyar zuciya, musamman wajen aike wa da jini a cikin sassan jikin mutum baki-daya. Haka zalika, kwanciya da bangaren hagu; na inganta wurare daban-daban a jikin Dan’adam tare da rage damuwa a zuciya, musamman ga masu fama da ciwon zuciya ko hawan jini.

LABARAI MASU NASABA

Yadda Na Tsira Daga Cutar Mashaƙo A Katsina: “Na Fara Da Tsartuwar Jini Tare Da Yawu”

2 – 3 Cikin 10 Na Masu Cutar Diphtheria Na Iya Mutuwa A Katsina – NMA

4-Yana rage ciwon baya: Ga masu fama da ciwon baya, kwanciya da barin hagu na taimaka musu wajen samun sauki. Kazalika, yana taimakawa wajen samun daidaituwar kashin baya.

5-Taimaka wa mai ciki yayin dauke da juna biyu: Galibi, a kan bai wa masu dauke da juna biyu shawarar kwanciya a bangarensu na hagu, saboda wasu kwararan dalilai. Kwanciya da wannan bangare, na kara yawan gudanar jini zuwa mahaifa tare da taimaka wa jariri wajen yin zagaye. Haka nan, yana kuma taimakawa rage lamba a kan hanta da koda tare da habaka aikin gabobi ga mai juna biyun da kuma jaririn nata.

6-Taimaka wa hanyoyin fitar fitsari da bayan gida: Ko shakka babu, kwanciya da barin hagu na inganta mugudanan ruwan jiki tare kuma da taimakawa wajen fitar fitsari da bayan gida.

7-Yana taimaka wa Saifa wajen saurin tace jini: Saifa, tana matukar taka rawa wajen tace jinin Dan’adam, wadda take a bangaren hagu a jikin mutum. Don haka, barci a bangaren hagu; yana kara saurin aikin Saifa wajen tace jini, sannan yana kara karsashin lafiya da kuma saurin tace jini yadda ya kamata.

8- Yana rage munshari a tsakanin ma’aurata: Kwanciya da bangaren hagu yana rage yawan munshari tare da kara dadin barci. Wannan bangare, na bude hanyoyin iska tare da rage yiwuwar bushewar makogwaro.

Kwanciya
Sani Anwar
+ postsBio
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    2027:Mata Shida Da Ke Takarar Neman Shugabancin Nijeriya
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    Dambarwa A Kasuwancin Iyalan Indimi
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    Illar Shan Taba Sigari Da Dangoginta
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    Abubuwan Da Ba A Faɗa Ba Game Da Auren Gata Da Gwamnatin Jihar Kano Ta Jagoranta

MASU ALAKA

Yadda Na Tsira Daga Cutar Mashaƙo A Katsina: “Na Fara Da Tsartuwar Jini Tare Da Yawu”
Manyan Labarai

Yadda Na Tsira Daga Cutar Mashaƙo A Katsina: “Na Fara Da Tsartuwar Jini Tare Da Yawu”

September 3, 2026
Kwanciya
Kiwon Lafiya

2 – 3 Cikin 10 Na Masu Cutar Diphtheria Na Iya Mutuwa A Katsina – NMA

August 30, 2026
Yadda Ake Zaɓar Jaririn Da Ake So A Haifa A Kimiyance
Kiwon Lafiya

Yadda Ake Zaɓar Jaririn Da Ake So A Haifa A Kimiyance

August 9, 2026
Next Post
Tsaftar Muhalli: Gwamnatin Nasarawa Ta Rufe Kasuwar Tumatir A Lafia

Tsaftar Muhalli: Gwamnatin Nasarawa Ta Rufe Kasuwar Tumatir A Lafia

LABARAI MASU NASABA

Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

September 9, 2026
An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

September 9, 2026
Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba

Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba

September 9, 2026
Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa

Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa

September 9, 2026
Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

September 9, 2026
Renon Matasa A Kan Kyakkyawar Turba Ginshiki Ne Na Gina KasaBy

Renon Matasa A Kan Kyakkyawar Turba Ginshiki Ne Na Gina KasaBy

September 9, 2026
Bikin CIFTIS Zai Ingiza Bude Kofa A Kasar Sin

Bikin CIFTIS Zai Ingiza Bude Kofa A Kasar Sin

September 9, 2026
“Ajin Tashar Sararin Samaniya Na Hong Kong Da Macau” Ya Kara Wa Matasa Sha’awar Kimiyya Da Karfafa Kishin Kasa

“Ajin Tashar Sararin Samaniya Na Hong Kong Da Macau” Ya Kara Wa Matasa Sha’awar Kimiyya Da Karfafa Kishin Kasa

September 9, 2026
’Yansanda Sun Cafke Matar Da Ta Kwara Wa Maƙociyarta Tafasasshen Ruwan Zafi A Abuja

’Yansanda Sun Cafke Matar Da Ta Kwara Wa Maƙociyarta Tafasasshen Ruwan Zafi A Abuja

September 9, 2026
Taron Kolin Urumqi Ya Mayar Da Hankali Kan Kwarewar Shugabanci A Xinjiang Da Muhimmancinta Ga Duniya

Taron Kolin Urumqi Ya Mayar Da Hankali Kan Kwarewar Shugabanci A Xinjiang Da Muhimmancinta Ga Duniya

September 9, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.