Baqeer Muhammad" />

Illoli Biyar Na Dumama Abinci A Injin ‘Microwabe’

Injin ya na da matukar sauri da sauki wajen dumama abinci, amma baa nan gizo ke tsakar ba, batun illolin injin shi ne abun da ya fi damun masana, in da suka gudanar bincike masu yawa akan illolin dumama abinci da injin, cikin an gano guda biyar da suka fi illa ga ‘yan adam.

1-Yana Kone Sinadaran Abinci: An tabbatar da cewa amfani da injin wajen dumama abinci ya na kone sinadarai masu amfani ga jikin mutum wanda suke cikin abinci, inji yana fitar da wani irin zafi mai karfi ta in da zafin yake kone ruwan cikin abincin don ya dumama shi a haka duk sinadarai masu gina jiki za su kone kurmus, ga dai abinci ana ci amma ba shi da wani amfani ga jikin mutum.

2-Yana Bata Madara Da Sinadarin (Bitamin B-12): sinadarin yana da matukar amfani wajen ba jikin mutum komari, ana samun sinadarin ne a cikin jan nama da madara, duk abinci da yake kunshe da wannan sinadarin in aka dumama shi da injin to ya zama shiririta saboda injin yana matukar kashe kwayoyin sinadarin da suke amfanar da jiki saboda tsabar tsananin karfin da zafin injin yake da shi.

3-Yana Tara Sinadarin “Carcinogen” A Jiki: sinadarin ya na da matukar illa in ya yi yawa a jikin mutum, duk abincin da aka dumama a leda ko roba to Carcinogen yana shiga cikin sa, in ana ci yau da kullum to zai taru a jikin mutum har ya kai matakin da zai ma mutum muguwar illa, wani kamfanin na kasar Rasha ne ya fara fitar da wannan binciken, inda ya nuna karfin zafin injin ya na sa roba ko leda su fitar da sinadarin na Carcinogen cikin abinci in da ana ci yana taruwa a jikin mutum a karshe zai yi mummunar illa a jiki.

4-Yana Canza Tsarin Jinin Jiki: sakamakon yawan amfani da injin wajen dumama abinci ya na jawo konewar kwayoyin jinin jikin mutum wato (blood Cells) Kenan, ya na kona jajayen kwayoyin jini (Red blood cells) kurmus, don haka fararen kwayoyin jini (white blood cells) za su karu a jikin mutum daga nan kuma kitse zai samu damar taruwa sosai, taruwar za ta yi illa sosai ciki har da jawo karancin jini da wasu cutuka.

5-Sun Sauya Yanayin Bugun Zuciya: yawan cin abincin da ake dumama wa a injin misali madara da ganye ya na jawo sauyi a yanayin bugun zuciyar mutum, tasirin wannan zafi mai karfi da injin yake fitarwa ya sa yawan cin abincin da aka dumama da inji yake da tasiri ga bugun zuciyar mutum, masana sun shawarci ma su tahammuli da inji su dinga lura sosai in sun ji yanayin bugun zuciyar su ya canza ko kuma yawan ciwon kirji to su yi maza su daina amfani da abincin da ake dumama wa da injin.

 

Exit mobile version