A kwanan baya ne wasu faifan Bidiyo suka karade shafukan sanda zumunta na zamani, kan batun yin sulhu da ‘yan bindiga daji da suka addabi wasu alumomin da ke a Jihar Katsina.
An gudanar da suhun ne, a tsankin shuwagannin wasu kananan hukumomin da ke a jihar ta Dikko.
- Manyan Jami’an Kasashen Afirka Suna Fatan Fadada Hadin Gwiwa Da Kasar Sin
- Dubban Matasan Kano Sun Yi Zanga-zangar Lumana Domin Goyon Bayan CP AI Bakori
Sai dai, wasu ‘yan Nijeriya sun yi suka kan kulla wannan yarjejiniyar ta yin suhun, inda itama wannan Jaridar, ta bi sahun masu yin sukar.
Ya zuwa yanzu, kananan hukumonin da suka kulla wannan yarjeniyar sun hada da, Jibia, Batsari, Safana, Danmusa, Kurfi, Musawa, Matazu, Faskari, Kankara, Dandume da Sabuwa.
Wasu daga cikin wadanda suka halarrci kulla yarjeniyar sun hada da, jami’an tsaro. Sarakunan gargajiya da kuma jami’an gwamnati.
Wani abu da ya ja hanklan mutane shi ne, irin muggan makaman da ‘yan bindigar suka hallara da su a wajen kulla yarjejeniyar, wadanda kuma babu wani mahaluki da ke da ikon kwace makaman daga hannunsu, a yayin kulla yarjejeniyar, ta jeka nayi ka.
Kazalika, a cikin daya daga cikin faifan Bidiyon, an ga yadda daya daga cikin shuwagabannin ‘yan bindigar ya yi bazaranar shedawa gwamnati da sauran jami’an gwamnatin da suka halarci wajen kulla sulhun cewa, idan har gwamnati ta kuskura ta kashe ‘yan bindiga dubu goma, suma za su hallaka adadin mutane kamar hakan.
Wasu ‘yan Nijeriya dai, sun yi ittifakin cewa, kasar nan, ta koma tamkar, a hanun tafin ‘yan bindigar.
Kulla wannan yarjeniyra dai, ta nuna a zahiri na irin gazawar da shuwagannin wadannan kananan kananan hukumomin na jihar ta Katsina.
Mun sha bayyana cewa, yin yarjejeniya da ‘yan bindiga ba a ba ce, da za ta kasance ta dogon zango ba.
Hujjar da zamu iya kafawa a nan ita ce, a lokacin mulkin tsohon gwamnan Jihar Katsina Aminu Bello Masari, tsohuwar gwamnatinsa ta yi sulhu da su, wanda har mazauninsu ya same su ya dauki hotuna tare da su da kuma raba masu da kudade, amma daga baya, abin da ya biyo baya shi ne, suka ci gaba da hallaka rayukan jama’ar jihar.
Bugu da kari, a Jihar Zamfara, a lokacin tsohowar gwamnatin gwamna Mohammed Matawalle wanda a yanzu shi ne, karamin ministan tsaro, ya bai wa ‘yan bindigar damar yi masu afuwa, duk da cewa, wadannan miyagun, sun hallaka rayukan jama’a da yi wa mata fyade da tarwatsa wasu al’ummomi daga garuruwansu da kuma sace dubban mutane.
Tsohuwar gwamnatin Matawalle, ta dauki wancan matakin ne, bisa yakinin cewa, ‘yan bindigar za su ajiye makamansu su kuma rungumi yin sulhu da gwamnatin, amma har yanzu, ba su dakatar da aikata ta’asar ta su ba, musamman duba da cewa, har yanzu jihar na ci gaba da fuskantar hare-harensu.
Hakazalika, gwamnan Jihar Katsina Dikko Umar Radda wanda ya gaji tsohon gwamann jihar Masari da kuma takwaransa na Jihar Zamfara, Lawal Dauda Dare, wanda ya gaji tsohon gwamnan jihar Matawalle, suka kesa kasa da cewa, atabau, ba za su kulla wata yarjejeniyar sulhu da ‘yan bindigar ba.
Sai dai, da alamu Radda ya sauya na sa ra’ayi, wanda hakan ya bai wa kananan hukumomin jiharsa su sha daya kulla yarjejeniyar da ‘yan bindigar domin samar da zaman lafiya, a tsakanin alumominsu.
A nan dai, koma dai menene ra’ayin mu a nan, wannan yarjejeniyar da ‘yan bindigar da suka dauki ran muane tamkar ba komai ba da karbar kudin fansa daga gun ‘yanuwan wadanda suka sace ‘yanuwansu da tarwatsa al’umomi daga muhallansu wannan ya nuna irin asalin gazawa daga bangaren gwamnatin jihar ta Katsina.
Har yanzu dai, akwai dimbin tambayoyi dangane da wannan yarjejeniyar ta jeka na yi ka, domin hakan ya nuna a zahiri na gazawar gwamnatin jihar na kare rayuka da dukiyoyin ‘yan jihar.
Matsayin a wannan Jaridar shi ne, yarjejeniyar da ‘yan bindigar aba ce da har yanzu ba ta sauya zani ba, kuma zai yi wuya hakan ta faru, domin a nan, muma bama goyon bayan hakan.
Shi ma wai, ta wacce fuska ce, za a kwantarwa ‘yanuwan wadanda ‘yan bindiga suka halka masoyansu da cin mutuncinsu da yi masu fyade da kuma aikata masu nau’ukan ta’asa da ban da ban.
Kazalika, wannan kulla yarjeniyar ta nuna irin gazawar da jami’an tsaro suka da ita ko da yake dai, wasu na yin tsegumin cewa, shiga aikin na tsaro tamkar ya koma ne wata hanya ta neman kudi a kasar.
A nan muna nuna damuwar da cewa, wannan kulla yarjejeniyar tamkar zuba kima da mutuncin Nijeriya ne, a idon duniya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp