Dan takarar Gwamnan Jihar Bauchi a zaben 2023 a jam’iyyar APC, Sadique Baba Abubakar, ya nuna kwarin guiwar cewa zai samu nasarar a kotun sauraren kararrakin zabe.
Abubakar ya ce a zaben da aka gudanar shi ne ya samu nasara kuma yana da tulin hujjojin da za su gabatar a gaban kotun sauraron kararrakin zabe da hakan zai kai a dawo masa da wadanda suka zabe shi kujerar.
- Ranar Ma’aikata: NLC Ta Bukaci Daidaita Albashin Ma’aikata A Kebbi
- NAFDAC Ta Haramta Shigo Da Indomie Saboda Zargin Sanya Ciwon Daji
A hirarsa da ‘yan jarida bayan dawowarsa daga tafiya a ranar Litinin a Bauchi, Sadique ya ce, sashin shari’a a kasar nan yanzu ya ingantu don haka yana da cikakken kwarin guiwar za su wanzar da adalci da gaskiya a tsakani.
“Nasara a hannun Allah ya ke. Mun tabbatar zalumci aka yi kuma da izinin Allah, Allah zai kwato hakkin jama’a. Sannan mun tabbatar yanayin shari’a na Nijeriya na da kyau don mutane ne adilai wadanda za su tabbatar da gaskiya.”
A cewarsa, “Muna godiya wa Allah (SWT) wanda ya ba mu dama muka dawo bayan mun fara wannan gwagwarmayar da muka sanya a gaba na tabbatar da cewa an kwato hakkin jama’a an maida musu.
“Wannan gwagwarmayar mun dauke shi kuma da izinin Allah, Allah zai ba mu nasara a kai.”
Ya gode wa jama’a bisa addu’o’in da ya ce sun yi masa musamman a lokacin azumi da kuma fatan alkairi da suke masa, kana ya kuma jinjina wa kokarin jam’iyyar APC da ta yi kuma take musu. Sai ya nemi masoya da magoya bayansa da su cigaba da kasance masu bin doka da oda har zuwa lokacin da kotu za ya saurari kararsa.
Abubakar ya tabbatar da cewa za su ci gaba da neman hakkinsu babu dare ko rana jar sai sun tabbatar sun kwace mulki, “Ina da kwarin guiwar Allah zai kwato wa jama’a hakkinsu domin Allah ya san abun da ya faru a lokacin zaben nan kuma mun tabbatar matakan da muka dauka za su fito da abubuwan da ake nema na ganin an kwato hakkin jama’a an dawo da shi.
“Na tabbatar da jama’anmu ba su bukatar cigaba da tsarin da ba a biyan albashi, tsarin da yara ke karatu a kasa alhalin ana nan ana gina manya-manyan ofisoshi na biliyoyi wanda ba shi ne ya dami al’umma ba.
“Saboda haka ganin yadda mutane suka ba mu hadin kai a ziyarar da muka kai kananan hukumomi muka ga ya wajaba a kanmu mu cigaba da wannan gwagwarmayar har sai mun tabbatar an kwato hakkin jama’a.”
Idan za ku tuna dai a zaben da aka fafata na 2023 da jam’iyyun siyasa daban-daban guda 14 suka shiga aka fafata da su, sakamakon ya nuna cewa Gwamnan da ke kan kujerar Bala Muhammad na jam’iyyar PDP ya samu nasarar tazarce da kuri’u 525, 280 yayin da abokin hamayyarsa na kusa-kusa Sadique Baba Abubakar ya tashi da kuri’u 432, 272 kamar yadda INEC ta shelanta. To sai dai Abubakar ya kalubanci sakamakon a gaban kotu.