Mai koyarda ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Chelsea, Antonio Conte ya bayyana cewa wani lokacin yanajin haishi idan yatuna cewa shi mai koyarwa ne.
Antonio Conte, ya ce yana son zama kusa da iyalansa domin samun farin ciki, amma hakan bazai kasance ba saboda koda yaushe tunaninsa yana fili.
Yace, abune mai wahala harkar koyarwa, saboda baka da lokacinka dana iyalanka wanda hakan ba ƙaramin matsala bane ga iyalanka da yan uwanka.
Ya cebabban burin mutum shine zama kusa da iyalai domin sune zasu saka farin ciki da kwanciyar hankali sannan kuma zaka manta da duk wata damuwa.
A kwanakin baya dai ya bayyana cewa bazai dade yana koyarwa a waje ba inda ya ce yana son komawa ƙasarsa ta italiya domin ci gaba da koyarwa.