Tsohon mataimakin shugaban kasa kuma wanda jam’iyyar PDP ta tsayar takarar kujerar shugaban kasa a zaben 2023, Atiku Abubakar, ya kira ga hukumar zabe da ta gaggauta sake sakamakon zaben gwamna a jihar Adamawa.
Atiku Abubakar, ya bayyana haka a wani taron manema labarai da ya kira a gidansa dake Yola, yace kiran ya zama wajibi, duba da yanayin da jihar ke kokarin fadawa sakamakon rashin bayyana jam’iyyar da ta lashe zaben.
A ranar Asabar, hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta gudanar da zaben kujerar gwamna a jihar, to sai dai hukumar zaben ta sanar da sakamakon zaben kannan hukumomi 20, bata sanar da na karamar hukumar Fufore ba.
Tsohon mataimakin shugaban kasar ya kara da cewa “tun a jiya da daddare na Kira shugaban hukumar zabe ta kasa, domin a sake sakamakon zaben.
“Mun yi zabenmu lami-lafiya, amma rashin bayyana sakamakon zabe zai haifar mana da matsa, ci gaba da rike sakamakon zaben shi yake kara fargaba da zaman dar-dar, kuma na gayawa shugaban hukumar zaben haka.
“PDP ta lashe zabe, sun dora a shafinsu don haka su sanar da sakamakon da suka Dora din, domin zaman lafiyar alummar Adamawa ya fiye mana komai.
“Ina kira ga INEC da masu ruwa da tsaki, da su sa baki domin samun zaman lafiya, an gudanar da zabe lafiya bai kamata a samu tashin hankali lokacin wajan bayyana sakamakon zabe ba” inji Atiku.
Sakamakon zaben karamar hukumar Fufore, ya rage hukumar zabe INEC bata sanar ba, kawo lokacin hada wannan rahoton