Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Ganduje, ya roki gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf da ya sauya sheka daga NNPP zuwa APC.
Da yake jawabi a taron masu ruwa da tsaki a Kano a ranar Alhamis, Ganduje, ya ce komarwa Abba jam’iyyar APC zai sa Kano ta zama jiha mai jam’iyya daya.
- Har Yanzu Auren Jinsi Haramun Ne A Nijeriya – ‘Yansanda
- Za Mu Dawo Da Martabar PDP A Katsina — Kwamitin Riƙon Ƙwarya
A cewarsa, APC ta kuduri aniyar zaburar da dukkan sauran kananan jam’iyyu don hadewa da APC a Kano.
Ganduje ya ba da tabbacin cewa jam’iyyar APC za ta samar da yanayi mai kyau ga Abba da kuma magoya bayansa wajen samu zaman lafiya da lumana a jam’iyyar APC.
“Mun samu nasara wajen jan hankalin wasu gwamnoni su dawo APC. Nan ba da jimawa ba wasu gwamnoni za su shigo jam’iyyarmu. To, idan za mu iya yin haka a matakin kasa, me ya sa ba za mu yi haka a matakin jiha ba?
“Kofarmu a bude ta ke. Muna gayyatar gwamnan Jihar Kano da ya bar jam’iyyarsa ta NNPP ya dawo APC.
“Mun yi alkawarin samar masa da yanayi mai kyau ga gwamnan Jihar Kano ta yadda ya dace.
“Wannan shi ne abin da ya dace tunda mu ne jiha mafi yawan jama’a a kasar nan,” in ji Ganduje.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp