Tsohon Shugaban Kasar Amurka, Barack Obama, ya roki ‘yan takaran zaben shugaban kasar Nijeriya tare da shugabannin jam’iyyun siyasa da su ba da gudumawa wajen ganin an gudanar da sahihin zabe cikin kwanciyar hankali a ranar Asabar.
A sakon da ya aike wa jama’ar kasar nan da ke shirin zuwa zabe, Obama ya ce Nijeriya ta fada cikin tsaka mai wuya amma kuma ta samu nasara a matsayin ta na kasa mafi karfin tattalin arziki a Afirka.
- Sauyin Kudi: Gwamnonin APC Sun Bukaci Buhari Da CBN Su Mutunta Umarnin Kotun Koli
- Dan Takarar Majalisar Tarayya Na Mazabar Wudil Da Garko A Jam’iyyar NNPP Ya Rasu A Kano
Tsohon shugaban, ya bayyana wannan zabe a matsayin wata damar rubuta wani sabon tarihi na ci gaban kasar nan ta fuskar siyasa, yayin da ya bukaci jama’ar Nijeriya da su jinjina wa kansu a kan wannan nasarar da aka samu.
Obama, ya ce ‘yan Nijeriya sun bayar da gudumawa wajen samun ‘yancin kai da kuma sanya kasar nan a kan tafarkin dimokuradiyya bayan kwashe dogon lokaci ana mulkin soja tare da kuma inganta rayuwa da gina tattalin arziki.
Haka zalika, ya ce yanzu wata dama ta samu na rubuta wani sabon babi dangane da zabe mai zuwa, kuma ana samun nasarar zabe ne idan an gudanar da shi ba tare da tunzura jama’a wajen tashin hankali ko kuma yin wani abin da zai kawar da sahihancinsa ba.
Obama ya yi kira ga daukacin ‘yan Nijeriya da su gudanar da zabukansu cikin kwanciyar hankali ba tare da samun wata tangarda ba.