Abba Ibrahim Wada" />

Ina Son Cigaba Da Zama A Real Madrid –Zidane

Mai koyar da ’yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid, Zinedine Zidane ya bayyana cewa, ya na son cigaba da koyar da kungiyar har zuwa kakar wasa ta gaba domin cigaba da samun nasarori.

Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid dai ta na matsayi na uku akan teburin laliga maki 15 tsakaninta da Barcelona wadda take mataki na daya akan teburin yayinda Atletico Madrid take mataki na biyu akan teburin.

A yanzu dai gasar zakarun turai kawai ya ragewa kungiyar ta Real Madrid ta laashe idan kuma bata iya lashe gasar ba to zata kammala kakar bana batare da kofi ko daya ba bayan da Barcelona tayi mata nisa sannan kuma akayi waje da ita a gasar cin kofin Copa Del Rey.

Real Madrid dai zata kai ziyara birnin Turin domin fafata wasan kusa dana kusa dana karshe da kungiyar kwallon kafa ta Jubentus a gasar zakarun turai sai dai zidane yace nasara a gasar zakarun turai ce kawai zata iya sawa yacigaba da aiki a kungiyar.

Ya cigaba da cewa tabbas yanason yacigaba da zama a kungiyar, kuma daman tun farko ya bayyana haka kuma bai canja ra’ayinsa ba amma dole sai yacika sharudan kungiyar wato cin kofin.

A karshe yace shekararsa 18 a kungiyar saboda haka kungiyar ta bashi dama yayi duk abinda yakeso kuma yanayi saboda haka idan aka tambayeshi cewa yanason cigaba da zama a kungiyar zaice Eh, saboda daman shine burinsa.

 

Exit mobile version