Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home ADABI

Ina Son Zama Farfesa, Cewar ’Yar Shekara 18 Da Ta Wallafa Littafi A Kebbi

by Sulaiman Ibrahim
January 4, 2021
in ADABI
3 min read
Zama Farfesa
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

MAIMUNA GARBA HAMMANI wata matsashiyyar yarinya ce ’yar Shekaru 18 da haihuwa a duniya, wacce ta wallafa littafin wakokin Turanci mai taken ‘I Shall Live My Season’ a Jihar Kebbi, inda ba da jimawa ba aka kaddamar da shi a Birnin Kebbi, babban birnin jihar. Wakilin LEADERSHIP A Yau, UMAR FARUK, ya zanta da wannan matashiyar marubuciyar kan burinta. Ga yadda zantawar ta kasance:

 

samndaads

Masu karatu na son sanin dan takaitaccen tarihinki?

An haife ni a ranar 27 ga watan Mayu na shekara ta 2002 a Birnin-Kebbi. Na yi karatun firamare da sakandare a kwalijen Higher Standard da ke a cikin garin Birnin-Kebbi, inda na kammala karatun sakandare a shekara ta 2020. Yanzu haka zan soma karatun digiri na farko a Jami’ar Gwamnatin Tarayya da ke Birnin-Kebbi, wato FUBK, inda zan karanta English Literature.

Me ya ba ki sha’awa ga rubuta wakokin Turanci da ake kira ‘poet’?

Alhamdulillah, mamata mai suna Hajiya Rafa’atu Noma Hammani ita ce ta ba ni kwarin gwiwar rubuta wadannan wakokin Turanci na ‘poet’, domin ita malama ce. Haka kuma kakata, Hajiya Maimuna M. Bala, ta gefen mamata, marubuciyar littafai ce. A kan haka ne na kara samun wasu dabaru na yadda ake rubuta wakokin Turanci na ‘poet’, ‘poem’ da kuma ‘poetry’, wanda ta haka ne na kwashe shekaru biyar kafin samun nasarar kammala rubuta wannan tallafi da na sanya wa suna ‘I Shall Libe My Season’.

 

Me littafin da ki ka rubuta ya ke koyarwa?

Ma sha Allah. Littafi ne na yabo ga wasu mutane da suka taimaka wurin ganin cewa na yi rayuwa irin wadda addinin Musulunci ya tanada, kamar mamata, Hajiya Rafa’atu Noma Hammani, babana, Garba Hammani, yayyena mata da maza, Gwamna Abubakar Atiku Bagudu da kuma kakata, Hajiya Maimuna M. Bala. Sauran sun hada da malamina da ke kula da ni yayin da na ke rubuta wadannan littafi, Malam Jalaludeen, malami a Jami’ar Gwamnatin Tarayya da ke a Birnin-Kebbi na sashen koyar da Turanci da sauransu.

Bisa ga hakan ne na ga bari na rubuta wakokin yabo ga wadannan mutane kan irin dawainiyar da suka yi ta yi da ni har zuwa inda na ke yanzu. Bayan na kwashe shekaru biyar Ina rubuta wadannan wakokin yabo sai aka bai wa Farfesa Bello Bada na Jami’ar Usmanu Danfodiyo da ke Sakkwato, domin yin bita kan kalmomin da na yi amfani da su da kuma yadda na tsara littafin, domin bada damar wallafa littafin, inda Farfesa Bello Bada ya gamsu da yadda na rubuta wadannan wakokin yabo ga wadannan mutane, domin wallafawa a cikin al’ummar. Daga nan iyaye na suka dauki nauyin tabbatar da cewa, an gudanar da taron bikin wallafawa wannan littafi, wanda aka kaddamar a dakin taro na Saffar Otel da ke Birnin-Kebbi. Haka kuma littafin nawa bai tsaya nan ba kawai; ya yi magana kan ilimin ‘ya’ya mata da kuma cin zarafinsu ta hanyar yi mu su fyade.

Bugu da kari, akwai wata yarinya ’yar shekaru bakwai da haihuwa a duniya da ake azawa talla, ba ta zuwa makaranta, wanda hakan ya sanya wani kawunta ya yi ma ta fyade, amma cikin iyawar Allah ta samu gata daga hukumar bada tallafi na asusun kananan yara, wato UNICEF, inda ta yi karatun da har ta samu nasarar zama likita. Wannan matsala ta yarinyar mai suna Talatu na daya daga cikin abin da ya sa na wallafa wannan tallafi da kuma matsalar bautar da ‘ya’ya mata da har tsallakawa ake yi da su zuwa wasu kasashe, wanda a turance ake Kira ‘Child’s trafficking’.

Wane irin darasi ki ke son ‘ya’ya mata su koya daga littafin ki ka wallafa?

Ina son ‘ya’ya mata su dogara ga kansu ta hanyar yadda da cewa ilimi makami ne kuma abin tinkaho ne, haka kuma yana da girma da daukaka a duk inda mutum ya ke. Har ila yau, su tabbatar da sun samu ilimin boko da na addini, domin rashin ilimin shi ne ke sa ana amfani da damar wurin cin zarafin ’ya’ya mata ta hanyar yi mu su fyade da kuma bautar da su ta hanyoyin da ba su dace ba.

 

Mene ne burinki?

Daya daga cikin abinda na ke da buri shi ne na kafa cibiyar tallafa wa karatun ’ya’ya mata a kasarmu ta Nijeriya in sha Allah.

 

Daga karshe meye fatanki a rayuwar a duniya? 

Fatana da kuma burina shi ne, na kasance malamar jami’ar, in yi karatu har na zama farfesar ta ‘literature’. Haka kuma kamar yadda na fada, Ina kuma da buri na kafa cibiyar tallafa wa karatun’ya’ya mata da kuma shiga cikin harakokin siyasa, domin na taimaka wa al’ummar a zaman rayuwata a duniya. Na gode.

SendShareTweetShare
Previous Post

Ziyarar Wang Yi A Kasashe 5 Na Afirka Tana Da Muhimmanci Sosai Ga Dangantakar Dake Tsakanin Sin Da Afirka A Shekarar 2021

Next Post

‘Okay’ Din Ciyaman, Sam Nda-Isaiah (3)

RelatedPosts

Fitattun Littattafan Hausa A 2020

Fitattun Littattafan Hausa A 2020

by Sulaiman Ibrahim
1 day ago
0

Masu iya magana suka ce 'komai ya yi farko zai...

Rayuwan Aurena

Sharhin Littafin: A Rayuwar Aurena: Abin Da Ba Zan Manta Da Shi Ba

by Muhammad
2 weeks ago
0

Na Adamun Adamawa Bauchi Daga Yusuf Kabir 09063281016 Sunan wannan...

Haduwar Jini

Haduwar Jini (4)

by Sulaiman Ibrahim
3 weeks ago
0

Bayan kwana daya da afkuwar hakan sai Salamatu kawar Lantana...

Next Post
Ta’aziyar Rasuwar Sam Nda Isaiah

‘Okay’ Din Ciyaman, Sam Nda-Isaiah (3)

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

Leadership Epaper
ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version