Hussaini Baba" />

INEC Ta Ba ‘Yan Majalisun PDP Na Jihar Zamfara Shedar Nasara Zabensu

Kwamishiniyar hukumar zabe mai zaman kanata ta jihar zamfara, Dakta Asama’u Sani Mai kudi ,karkashin jagorancin hukumar subi umarnin koton koli ta bada na baiwa ‘yan Majajalisun Dokokin jihar zamfara,na jamiyyar PDP ta kardar cin zaben tun tanar 24/5/2019.da kotun ta bada su umarni.sai yau juma’ane hukumar ta mikamsu takardun hannu da hannu.

‘Yan majasun su Ashirin da hudu ne ,Ashirin da uku daga jamiyyar PDP su ke sai kuma guda daya, Honarable Kabiru Hashimu daga Jam’iyyar NRM.

Kwamishiniyar Dakta Asamu ta bayyana godiyar ta da hadinkan da jajurcewa da masu ruwa da tsaki suka bayar dan ganin ansamu cigaban mulkin demokwaradiya .wadanda suka hada da Hukumar wayar da kai ta kasa watau NOA,’Yan jaridu, Jami’an tsaro, Sarakuna da Malaman addini, ‘yan siyasa da kungiyoyi masu zaman Kansu dukkansu sun ba da gagarumar gudummuwa wajen tafiyar da wannan zabe muna godiya.

Dakta Asama’u ta yi kira ga ‘yan majalisun da su tashi tsaye wajen samar wa al’ummar jihar Zamfara ci gaban rayuwa,dan samun roman dimokaradiyya .

A nasa jawabin Mataimakin Gwamnan jihar zamfara, Baban bako, Hon Mahadi Aliyu Gusau ya bayyana godiyar sa ga Allah da samun nasara wannna zaben da kuma su kanasu ‘yan majalisun ,su zamo masu San ci gaban al’ummar jihar Zamfara da samarwa al’ummar dokokin da za su ciyar da jihar Zamfara gaba.

Exit mobile version