Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta yi kira ga jam’iyyun siyasa, ‘yan takara, da magoya bayansu da su wanzar da zaman lafiya a zaben gwamnan Jihar Ondo da za a yi a ranar 16 ga watan Nuwamba.
Shugaban hukumar INEC na kasa, Farfesa Mahmood Yakubu ne ya yi wannan roko a lokacin da yake sa ido a kan taron fara shirye-shiryen zaben gwamnan Jihar Ondo na shekarar 2024, daukacin sassan jihar.
- An Kafa Kawancen Hadin Gwiwar Taron Masanan “Global South”
- Yadda Gwamna Nasir Idris Ya Daura Damarar Bunkasa Ilimi A Jihar Kebbi
Shugaban hukumar INEC wanda ya ce aikin fara shirye-shiryen na matsayin zakarar gwajin dafi kan tsarin zaben, ya ce idan jam’iyyu da magoya bayansu suka tabbatar da zaman lafiya zai bai wa hukumar damar gudanar da zabe na gaskiya da adalci.
A cewarsa, “Za mu tabbatar da cewa an bude dukkan rumfunan zabe a kan lokaci domin ka da masu kada kuri’a su zo su jira jami’an INEC da kayan zabe. Mun gwada ingancin na’urar, ba a tabbatar an tura kayayyakin zabe a kan lokaci.
“Muna yin iya kokarinmu a matsayin hukumar zabe da sauran su ma su yi nasu iya bakin kokarinsu, musamman jam’iyyun siyasa da ‘yan takara. Ina so in yi kira ga jam’iyyun siyasa, ‘yan takara da magoya bayansu da su tabbatar da cewa sun kiyaye zaman lafiya, wanda zai ba mu damar gudanar da zabe cikin lokacin da ya dace da kuma kammala ayyukanmu kan lokaci.
“Sannan kuma a sanar da al’ummar Jihar Ondo su fito kwansu da kwarkwatansu su zabi ‘yan takarar gwamnansu ranar Asabar.
“Ba za a samu jinkiri wajen gudanar da zaben, kuma zan zo tare da iyalina don kada kuri’armu ga dan takarar da muke son zaba,” in ji shugaban INEC.
Har ila yau, Adebimpe Bankole, wanda ya aka tantance a makarantar firamare ta Alagbaka, Akure a rumfar zabe ta 5, ya bayyana cewa INEC ta cancanci yabo domin ta gudanar da kashi 80 bisa 100 na wannan aikin zabe.
Bankole ya ce; “Na gamsu da tsarin saboda ban bata wani lokaci ba kafin a tantance in. Sai dai kuma ba zai iya ba su kashi 100 ba. Na dai ba su kashi 80 bisa 100 saboda sun yi kokari sosai. Da yardar Allah zan fito a ranar Asabar 16 ga watan Nuwamba domin in kada kuri’ata.”
Shugaban INEC tare da sauran jami’an hukumar, sun ziyarci Idanre, Ile-Oluji/Oke-Igbo, duka a gundumomin Ondo ta tsakiya da kuma Ondo ta Kudu a Jihar Ondo.