Idris Aliyu Daudawa" />

INEC Ta Horas Da Ma’aikata 814,453 Don Gudanar Da Zabe Mai Zuwa

Hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta dauki ma’aikatan wucin gadi 814,453 wadanda za su mata yi aikin zabubbukan shekara ta 2019 .
Hakanan ma Hukumar ta bayyana cewar zabubbukan shekara 2019 za su kasance sune zabubbukan da Hukumar zata yi, wadanda kuma, da akawai kyakkyawan zato na al’ummar duniya akan yadda shi al’amarin zai kasance cikin zaman lafiya sai kuma dangane da kayayyakin aikin da kuma, bangarenmatakan tsaro. Zaben shi ne babba wanda za’a yi shi cikin rana daya tun shekarar 1999 da masu zabe milyan 84, sai kuma jam’iyyun siyasa 91 . Ga kuma ‘yantakara 23,213 wadanda suke fafutukar samun mukamai 1558 abin da kuma ya shafi jami’an zabe fiye da 814,000.
Da yake yi ma wadanda suka taba Shugabancin Nijeriya tsofaffi da kuma wanda ke kan gado yanzu jawabi lokacin da aka yi taron majalisar kasa ranar Talata, Shugaban Hukumar Farfesa Mahmood Yakubu, wanda ya bayyana cewar dukkan kasafin kudin da suka kamata,an bata, inda kuma ya kara cewar zabubbukan shekarar 2015 , wani babban al’amarin ne wanda ya shiga tarihin siyasar Nijeriya.
Ya ci gaba da bayanin cewar “ Hukumar ta san jan aikin da yake gabanta dangane da al’amarin zabubbukan shekara ta 2019, ba zata sa ido tana gani ba, ta bari wasu suyi kokarin kawo cikas, lokacin da ake gabatar da zabubbukan domin kare martabar mulkin farar hula kamar dai yadda Yakubu ya jaddada”.
Shugaban Hukumar zaben mai zaman kanta INEC wanda yace, sai da suka tantance daga nan kuma suka dauki ma’aikatan wucin gadi 814,453 wadanda za su yi aiki lokacin zabubbukan, za kuma a fara horar dasu ranar 23 ga watan Janairu 2019.
Shugaban Hukumar zaben Yakubu wanda kuma har ila yau wanda shine Shugaban al’amuran zabe na kungiyar kawance ta kasashen yammacin Afirka (ECONEC) ya bayyana za ‘a yi amfani da tsarin da aka yi na, yadda za’a rarraba kayayyakin da suke da muhimmanci cikin sauri, wadanda suka hada da takardun da za’a zabi ‘yantakarar da ake so, da kuma takardar da za a rubuta sakamakon zabe na ko wacce rumfar zabe.
A lokacin har ila yau shi Shugaban Hukumar ya bayanna ma su mambobin majalaisar ta kasa, wata yarjejeniya da ita Hukumar ta zabe mai zaman kanta, ta cimmawa da kuma sa hannu da Kungiyar direbobi ta kasa NURTW , akan yadda za ‘a rika kai ma’aikatan zabe da kuma kayayyakin aiki, a lokacin da ya kamata ba kuma tare da wata matsala ba.
“ Hakanan ma kamar yadda ya kara bayani kasafin kudin Hukumar an sakar mata shi na Naira biliyan N189.8.”
Maganganun da Yakiubu ya yi sun kunshi al’amuran wuraren da za ayi zabe yadda aka gabatar da su zabubbukan da kuma yadda aka gabatar da shi zaben, da kuma duk wasu abubuwan da suka gudana lokutan daza ‘a yi zabubbukan,. sai kuma wadansu abubuwan da za’a ci gaba da yin su, dangane da shi zaben. Ga kuma al’amarin ci gaba da rajistar masu zabe, ga kuma amsar katinan zabe, yadda jam’iyyun siyasa za su ci gaba da tafiyar da harkokinsu, zabe, al’amuran tsaro, yadda masu ruwa da tsaki za su kasance cikin harkar ta zabe, kayayyakin zabe, da kuma abubuwan da ita Hukumar ta yi ta banagaren zabe, da kuma wayar da kan masu zabe, wanda kuma ya ce ma’aikatan Hukumar suna yin iyakar kokarin su.
Bugu da kari ya kara jaddada cewar Hukumar tayi wani aiki wanda kuma ya danganci shi tafiyar da ayyukan zaben, daga ranar 1 ga watan Yuni na shekarar 2018 zuwa 9 ga watan Janairu 2019 a, inda kum kuma ya kara cewar harka da kungiyoyin tsaro na ICCES da banagaren kasa, jihohi da kuma kananan Hukumomi,, saboda a duba wasu abubuwan da suka iya kawo barazana dangane da al’amuran tsaro lokacin zabe .
Ya ci gaba da bayanin cewar jami’an tsaro dangane harkokin zabe ana horar dasu, yayin da kuma samar da shi tsaron, ana ci gaba da daukar matakan, da Hukumomin tsaro saboda su samu bayar da tsaron lokacin zabe.
“ Gabatar da sahihin zabe wanda aiki ne na Hukumar da take kulawa da yadda ake aiwatar da su zabubbukan, sai kuma rarraba su kayayyakin zaben, da kuma kare yadda ake rarrabu su kayayyakin da kuma yin al’amura cikin adalci. Hakanan kuma ita Hukumar zabe zata gabatar zabubbuka kamar yadda dokar tsarin mulki ta dora mata.”
“INEC a shirye take kuma ta dauki niyya ta yin al’amuranta babu cut aba kuma cutarwa, ba kuma tare da wani nuna bambanci ba tsakanin su ‘yan takarar.
Sauran ayyukan hudu da suka rage a tsare-tsaren lokacin da za’a yi su, sun hada da, buga sunaye na ‘yan takarar gwamna, da kuma ‘ykan takarar majalisun jihohi,, sai kuma yadda za’ayi zaben ranar 16 ga watan Fabarairu, yayin da kuma na gwamnoni da ‘yan majalisun jhohi ranar 2 ga watan Maris.
“INEC ta san muhimmanci wadanda suke da ruwa da tsaki, saboda samun inganci al’amuran zabe, da kuma siyasa, wannan yana faruwa ta yin tarurruka aka-akai, da jam’iyyun siyasa, kungiyoyi masu zaman kansu, sai kuma kafofin yada labarai. Sai kuma tarurruka da ma’aikatu da kuma Hukumomi kamar su NYSC, FRSC, FIRS, EFCC, ICPC, NpopC, NIMC NCC dfa kuma NigComSat. Suma masu sarautun gargajiya ba’a barsu a baya ba, da kuma Shugabanni na kasa jihohi da kuma kananan Hukumomi.
Sai kuma al’amarin hadingwiwa da kasashen duniya sai kuma aboknin ci gaba, kamar su majalisar dinkin duniya, banagaren tsare- tsaren ci gaba, gidauniyar kasa da kasa saboda taimaka ma al’amarin zabe, kungiyar tarayyar Turai bangaren tallafawa harkokin zabe, da kuma sauran wasu kungiyoyi daban daban.

Exit mobile version