Wasu masu kaɗa ƙuri’a daga yankin mazabar Kogi ta tsakiya sun miƙa takardar ƙorafi ga hukumar zaɓe ta ƙasa (INEC) domin fara tsarin tsige Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan daga majalisar dattawa.
Takardar korafin na ɗauke da sa hannun jagoran masu buƙatar kiranyen, Salihu Habib, kuma an miƙa ta a shalƙwatar INEC da ke Abuja a ranar Litinin, 24 ga Maris, 2025.
- Kamfanin Kasar Sin Zai Gudanar Da Aikin Farfado Da Muhallin Halittu Na Kogin Nairobi Na Kasar Kenya
- Jakadan Sin A Amurka: Mayar Da Karin Haraji Makami Kaikayi Ne Da Zai Koma Kan Mashekiya
A cewar masu ƙorafin, waɗanda ke ƙarƙashin ƙungiyar Concerned Kogi Youth and Women, sun bayyana cewa sun yanke ƙauna kan Akpoti a matsayin wakiliyarsu, suna zarginta da cin zarafin ofis, da rashin biyayya ga ƙa’idojin aiki, da kuma rashin mutunta shugabannin majalisa. Sun buƙaci INEC da ta gaggauta fara aiwatar da tsarin amsar kiranye bisa tanadin sashe na 69 na Kundin tsarin Mulkin 1999 da kuma ƙa’idojin INEC.
Masu ƙorafin sun yi ikirarin cewa fiye da rabin masu kaɗa ƙuri’a a Kogi ta tsakiya sun rattaba hannu a takardar, inda suka ce ba zasu iya ci gaba da kasancewa ba tare da wakilci a majalisar dattawan ba. Wani mamba daga cikin masu ƙorafin, Uwargida Charity Omole, ta ce suna son a bi doka ne domin su samu sabon wakili da zai kare muradun al’ummarsu.
Habib da sauran masu ƙorafin sun musanta zargin cewa tsohon Gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello, ne ke ɗaukar nauyin wannan yunƙuri. “Bello baya nan. Mu ne ke nan,” in ji shi. INEC dai ba ta fitar da wata sanarwa ba har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, yayin da ake sa ran za a duba takardar bisa tanadin dokar ƙasa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp