Yayin da shekara ta 2024 ke ban kwana, tashe-tashen hankula da fitintinu na ci gaba da kazancewa. Shi kuma tattalin arzikin duniya yana ci gaba da tangal-tangal. Matsalar tsaro kuwa, wadda ta hada da ayyukan ta’addanci ta ki ci ta ki cinyewa, ballantana tabarbarewar yanayi wanda yake haddasa ambaliya, gobarar daji da dumamar yanayi, abin ba’a magana.
Wannan gagarumin kalubale ya sanya kasashe masu tasowa kasa cimma muradin Majalisar Dinkin Duniya (UN) na samu ci gaba mai dorewa ya zuwa shekara ta 2030. Wasu kasashen duniya kuwa, sabo da nuna isa da gadara, sun kekashe kan tsohon tsarin da suke a kai domin kare muradunsu na son zuciya.
- Kebbi Da Brazil Zasu Yi Haɗin Gwuiwa Kan Sarrafa Nama Ta Hanyar Zamani
- Kebbi Da Brazil Zasu Yi Haɗin Gwuiwa Kan Sarrafa Nama Ta Hanyar Zamani
Kasar Sin, wadda tun fil azal ba ta yarda da cin zalun ba, ko nuna fin karfi domin biyan bukatunta, tana nan ba ta canza ba a kan manufarta ta gujewa tsoma baki a cikin harkokin cikin gida na kasashen da take ma’amala da su. “Cude ni in cude ka” shi ne babban tafarkin da kasar Sin take a kai a ma’amalarta da sauran kasashen duniya.
Idan ba’a manta ba dai, a watan Satumban wannan shekara ne Beijing ta shirya ta kuma aiwatar da gagarumin taron koli na hadin gwiwa tsakanin China da kasashen Afirka. A wajen taron ne, wanda ya samu halartar shugabanni da wakilan gwamnatocin kasashen Afirka su 53, har da shugaban kungiyar tarayyar Afirka, AU, aka cimma matsaya ta bai daya ta zurfafa dangantaka tsakanin China da Afirka, bisa tsarin ci gaban duniya.
Dukkan mahalarta taron bakinsu ya zo daya ta fuskar hada karfi domin aiwatar da tsarin daidaito, bin ka’ida da kuma bunkasa tattalin arzikin duniya, ta yadda kowa zai amfana.
Dalilin gagarumar nasarar taron koli na Beijing shi ne bayanin da China ta yi dalla dalla ba tare da rufa-rufa ba a kan manufarta ta kulla wannan dangantakar hadin gwiwa tsakaninta da kasashen Afirka. Hakan ya gamsar da mahalarta taron, kasancewar sun fahimci cewa kowa zai ci gajiyar wannan hadin gwiwa. Wannan ne ya ba su kwarin gwiwar sakin jiki tare da samun natsuwa da mahukuntan kasar ta China a matsayin aminai na gaskiya.
A watan Nuwamban da ya gabata ne, aka gudanar da taron koli na kungiyar hadin kan tattalin arziki na kasashen duniya da ake kira G20 a birnin Rio de Janeiro na kasar Brazil. Taron shi ne na farko tun lokacin da kungiyar tarayyar Afirka (AU) ta samu kasancewa mamba a cikin kungiyar biyo bayan taron kungiya ta G20 karo na 18 da aka gudanar a birnin New Delhi na India a watan satumban 2023, kungiyar AU ta samu shiga cikin kungiyar G20 a hukunce.
China ita ce ta yi ruwa ta yi tsaki wajen ganin kungiyar AU ta samu shiga kungiyar G20, sannan kuma ta tsaya tsayin daka wajen ganin kungiyar AU ta taka rawar gani a harkokin shugabanci na duniya.
Wannan shi ne ya kara jaddada kalaman shugaba Xi Jinping na kasar Sin na cewa babu yadda za’a samu ci gaba da daidaito a duniya yayin da masu hannu da shuni suke kara azurcewa, su kuma talakawa suke kara durmuyewa cikin kangin talauci.