Khalid Idris Doya" />

IPOB Na Yunkurin Haifar Da Wani Yakin Basasa – Gwamnonin Kudu Maso Gabas

Gwamnonin Kudu Maso Gabas

Gwamnonin jihohin Kudu Maso Gabas sun gudanar da wani taron ganawa ta musamman da takwararsu na Ribas, Nyescom Wike a daren ranar Lahadi inda suka gargadi kabilar Igbo musamman ‘yan kasuwa da masu kamfanoni da su yi hattara da taka-tsantsan da haramtacciyar kungiyar masu fafutukar kafa yankin Biafra wato (IPOB).

Gwamnonin da suka halarci ganawar wacce ta gudana a gidan gwamnatin Fatakwal wanda shugaban kungiyar gwamnonin Kudu Maso Gabas Dabid Umahi of Ebonyi ya jagoranta.

Shugaban al’ummar Ohanaeze Ndigbo, Chief John Nnia Nwodo, shine ya jagoranci ‘yan bangarensu a yayin wannan zamar da aka zauna domin gano gaskiyar zargin da ake yi na kisan da wasu mambobin IPOB suka yi wanda suka labe da sunan zanga-zangar EndSARS.

Gwamna Umahi ya gargadi al’ummar Igbos da cewa su yi matukar taka-tsantsan da ‘yan IPOB, yana mai cewa kungiyar tana kokarin assasa wani yakin basasa ne.

Gwamnan ya ce sun halarta a jihar Ribas ne domin tattauna zarge-zargen da ke yada wa a kafafen sada zumunta na zamani da ke cewa ana kashe al’ummar Igbo a jihar.

Ya ce, bayan zaman da suka yi, sun gano zargin bai da tushe balle makama inda ya ce sam babu wani kisan ‘yan Igbo da ake yi a jihar.

Gwamna Umahi ya ce bayan ya saurari jawabin gwamna Wike kan aika-aikar da ‘yan IPOB suka aikata a Oyigbe wanda har hakan ya sanya aka sanya dokar hana zirga-zirga a fadin karamar hukumar, ya zama dole Igbo su nisanta kansu daga kungiyar IPOB.

Gwamnan ya ce abun kaito ne har ‘yan IPOB suke iya ikirarin cewa jihar Benue da Ribas suna iya daga tutarsu suna kuma nuna cewa su ‘yan kabilar Igbo ne.

Yana mai cewa akwai bukatar shugabanin Igbo su fito su nisanta kansu daga kungiyar IPOB gaba daya.

Ya ce, akwai bukatar masu ruwa da tsaki su hada kai wajen tabbatar da zaman lafiya a jihohinsu ba tare da biye wa wasu tsiraru suna kawo cikas ga lamura ba.

Tsohon gwamnan jihar Rigas, Dr Peter Odili, ya jinjina wa shugabanin Igbo a bisa shirye-shiryensu na tabbatar da zaman lafiya da har hakan ya kaisu ga ziyarar Wike da ya nuna hakan a matsayin wata hanya da za ta bada dama a samu nasarar shawo kan matsaloli da daman gaske.

A yayin zaman an jinjina wa matakan da gwamna Wike ke dauka na tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a jiharsa.

Wadanda suka halarci zaman sun hada da gwamnan jihar Abia Okezie Ikpeazu; mataimakin gwamnan jihar Anambra Nkem Okeke, Chief Emmanuel Iwuanyanwu.

Sauran jigajigan da suka halarta sun hada da mataimakin gwamnan jihar Ribas Dakta Misis Ipalibo Harry Banigo; tsohon gwamnan jihar Ribas Sir Celestine Omehia; sarakunan gargajiya na jihar Ribas; Amanayanabo na Opobo, King Dandeson Douglas Jaja da kuma shugaban jam’iyyar PDP na kasa Uche Secondus hadi da wasu kusoshi.

Exit mobile version