Iran Ta Musanta Harbo Jirginta Daga Amurka

Ministan harkokin wajen Iran Muhammad Jabad Zarif ya ce babu gaskiya cikin ikirarin da Amurka ta yi na harbo wani jirgin leken asirinta maras matuki a mashigin ruwan Hormuz.

Jabad Zarif ya bayyana haka ne bayan isa zauren majalisar dinkin Duniya don ganawa da babban sakatarenta Antonio Gutterresh.

A shekaran jiya Alhamis shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da cewa dakarun kasar sun harbo jirgin leken asirin na Iran, bayan da ya ketara iyakar da ke tsakaninsu a mashigin ruwan Hormuz.

A makwannin baya Iran ta taba kakkabo irin jirgin leken asirin na Amurka maras matuki, bayan ketara kan iyakarta da ta ce yayi, zargin da Amurka ta musanta a wancan lokaci tarkacen jirgin da Iran ta gabatarwa manema labaren kasar ta.

Iran ta musunta ikirarin da Shugaban Amirka Donald Trump ya yi cewar wani jirgin ruwa na yaki na Amurka ya kakabo wani jirgin Iran marasa matuki.

Kamfanin dilancin labarai na Iran Tasnim ya ambato kakakin rundunar sojojin Iran din Janar Abdolfazi Sekarchi yana mai cewar dukkanin jiragensu mara matuka da suka tura shawagi  a mashingin Ormuz da ke a yankin Gulf sun dawo lami lafiya.

Mashigin na Detroit Ormuz wanda a nan kusan kishi daya na man fetir da ake jigilarsa a duniya ya ke bi, ya kasance wani abin rikici tsakanin Amirka da Iran wanda kowane ke kara jige sojojinsa a gewayen mashigin.

Exit mobile version