Rahotanni sun nuna cewa, yarjajjeniyar Nukiliyar Iran ta fara tangal-tangal, bayan da Shugaban Amurka Donald Trump ya ƙi tabbatar da sahihancinta. A gefe guda kuma Iran na barazanar mai da martani mai tsauri.
Bayan da Shugaba Donald Trump ya ce Iran ba ta kiyaye lamirin yarjajjeniyar da ta rattaɓa hannu a kai da manyan ƙasashen duniya, sai ya bayyana wasu matakai masu tsauri da zai gindaya ma ta, ciki har ƙarin takunkumi da zummar daƙile niyyar gwamnatin Iran ta ƙirƙiro makaman Nukilya.
“Yau, ina mai shelar wasu matakanmu da wasu hanyoyi daban-daban da za mu yi amfani da su wajen tinkarar take-taken takala na gwamnatin Iran, kuma saboda mu ga cewa har abada, haƙiƙa ina nufin har abada Iran ba ta mallaki makamin Nukiliya ba,” a cewar Trump a wani jawabinsa da aka yaɗa daga Fadar White House ga ƙasa baki ɗaya, ta gidan talabijin.
Hasali ma, kiris ya rage ya tsame Amurka daga yarjejjeniyar ta 2015 da aka cimma tsakanin Iran, da ƙasashe masu kujerun dindindin a Majalisar Ɗinkin Duniya da Jamus da kungiyar Tarayyar Turai.
Ministan Harkokin Wajen Iran, Mohammed Jaɓad Zarif, ya yi barazanar abin da ya kira, “martani mai tsanani” muddun Trump ya ayyana Iran a matsayin marar kiyaye yarjajjeniyar. Wani mai magana da yawun rundunar sojin Iran kuma ya kara da cewa idan ta kama, sojojin ƙasar za su koya ma Amurka darasi.
Wani rahoto da ya sha banban da wannan kuma, ya yi nunu da cewa,manyan ƙasashen duniya sun mayar da martani ga shugaban Amurkan, in da suka ce za su ci gaba da mutunta yarjejeniyar Nukiliyar Iran bayan ya yi barazanar kekketa ta.
A wani kakkausan jawabi da ya gabatar a fadar White House, Mr. Trump ya caccaki yarjejeniyar wadda ta samu goyon bayan ƙasashen Birtaniya, Faransa, Jamus, Rasha da kuma ƙungiyar Tarayyar Turai.
Manyan ƙasashen sun ce, yarjejeniyar wani ɗangare ne na tabbatar da tsaro a ƙasashensu kuma za su ci gaba da mutunta ta.
Mr. Trump ya zargi Iran da tallafa wa ayyukan ta’addanci a yankin gabas ta tsakiya, yayin da ya buƙaci sake ƙaƙaba wa ƙasar takunkumi.
A cewar Trump, tuni Iran ta karya ka’idojin yarjejeniyar Nukiliyar da aka ƙulla a shekarar 2015, amma hukumar da ke sanya ido kan makamnin Nukiliya ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce, Iran na mutunta sharuɗan da aka gindaya mata.
A wani jawabinsa da aka watsa ta kafar talabijin a ranar, shugaban Iran Hassan Rouhani ya ce, suna mutunta sharuɗan yarjejeniyar, in da ya zargi Trump da furta kalamai marasa tushe.
Yanzu haka dai, Majalisar Dokokin Amurka na da kwanaki 60 don yanke shawarar janye wa daga yarjejeniyar ta hanyar sake ƙaƙaba takunkumi ga Iran bayan Trump ya ƙi sanya hannun da zai tabbatar wa Majalisar cewa, ya gamsu cewa, Iran na mutunta sharuɗan.