A yayin da ya shafe makonni biyar a kan karagar mulki, Shugaba Bola Ahmed Tinubu yana da wani muhimmin babban aiki a gabansa na kafa majalisar ministoci a matsayinsa na shugaban kasa shi ne.
A yanzu haka dai, Shugaban Tinubu yana da tsawon kwanaki 30 na kafa majalisar manistocin. Majalisa ta tanadi tsawan kwanaki 60 ne ga sabon shugaban kasa da gwamnoni su kafa majalisar zartarwa, amma tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya shafe watanni shida kafin ya nada ministoci a gwamnatinsa, wanda hakan ya saba wa ka’ida na kafa majalisar ministoci.
Bugu da kari, al’amura sun yi yawa matuka, kuma ‘yan Nijeriya sun lura cewa rashin samun nasarar dimokuradiyya ta hanyar ingantaccen tsarin mulki na gaskiya na iya kawo cikas ga makomar kasar a matsayin dunkulalliyar kasa.
A matsayinsu na manyan mambobi na majalisar ministoci da shugaban kasa zai nada kuma majalisar tarayya ta tabbatar da su sun kasance wani bangare na manufofi da tsare-tsare na zartar da hukunci da ke tafiyar da mulki yadda ya kamata.
Dole ne nadin nasu ya kasance mai cike da da’a da za su iya fidda kitse daga wuta. A wannan gaba, ana bukatar samun nagartattun mutane da za su iya taimakon shugaban kasa wajen sauke nauyin da ya rataya a wuyansa. A bisa ka’idodi sun nuna samun majalisar ministoci nagari na iya shafar makomar kowacce kasa.
Dangane da haka ne rahotanni ke cewa Shugaba Tinubu na neman masana a ciki da wajen kasar nan domin su taimaka masa wajen samun nasarar gwamnatinsa.
A yau, akwai sassa takwas masu matukar muhimmanci da za su iya haifar da sauye-sauye na kasa ko su iya rage radadin zamantakewa da siyasa da tattalin arziki a kasar nan. Wadannan sun hada da tsaro, wutar lantarki, ilimi, kiwon lafiya, noma, aikin yi da kuma samar da muhimman ababen more rayuwa. Idan aka mayar da hankali kan wadannan muhimman bangarorin za iya kawo sauyi ga kasa.
Bayan nada manyan mukaman hafsoshin tsaro, akwai ministoci da za a nada a cikin majalisar zartarwar Tinubu. Tun da akwai jihohi 36, kowace jiha sai an samu wakilcin akalla mutum daya ko fiye da haka, yayin da wasu za su samu mukamin babban minista, wasu kuma su kasance kananan ministoci.
Ko shakka babu shugaban kasar na da ‘yancin nada majalisar ministocinsa kamar yadda tsarin mulki ya tanada. A wurin nada mukaman minista, akwai abubuwan da yaka mata shugaban kasa ya yi la’akari da su wajen dauko mutanen da suka cancanta.
Duk da cewa dole ne Shugaba Tinubu ya bi tsarin daidaito wajen nada mukamai a gwamnatin tarayya, wanda ke bukatar minista daya daga cikin jihohi 36, zai iya tankade da rairaya a tsakanin masu fasaha da ’yan siyasa. Babban abin da ake bukata wajen zaben ministocinsa shi ne, cancanta ba tare da nuna son rai ko raja’a ga jam’iyya ba.
An saba mafi yawanci ‘yan siyasa ne ake bai wa mukaman ministoci duk da cewa ana sirki da ma’aikata da kuma kwararru daga bangarori daban-daban.
A halin da kasar nan ke ciki, mafi yawancin ‘yan Nijeriya na tsammanin shugaban Tinubu ya nada ministocin da suka dace ba tare da nuna bambancin siyasa ko ta jam’iyya ba.
‘Yan Nijeriya na son ganin sauyi a kan ministocin baya domin samun nasarar gwamnati yadda ya kamata.
Tuni dai ana ta yada jita-jitar cewa wasu mutane suna ci gaba da kamun kafa tare da bayar da cin hanci domin a ba su mukaman ministoci a gwamnatin Tinubu. Hakan yana matukar tayar da jijiyar wuya, inda da yawa ke ganin cewa ya kamata shugaban kasa ya tsaya ya darje wadanda zai nada a matsayin ministoci domin samun nasarar gwamnatinsa.