Tsohon shugaban kasa na mulkin soja, Ibrahim Badamasi Babangida ya bayyana irin shugaban kasan da ya dace da Nijeriya a 2023. Ya dai bayyana irin shugaban kasan da ya dace da Nijeriya a 2023 ne a wani tattaunawa da Jaridar Daily Trust ta yi da shiga.
Ya ce, “Ba wai wanda na saka a zuciya shi ne zai iya ba, mutumin da zai iya shi ne wanda yake da wasu abubuwa wadanda suka hada da ya kasance dan Nijeriya, dan siyasa ba kuma tsoho kamar ni ba.
Ya kuma kasance ya san yadda kasar take ciki a halin yanzu wanda zai iya tattaunawa da mutane kan matsalolin da ake damun su tare da daukan shawara a matsayinsa na shugaban kasa da yin aiki kafada da kafada da kungiyoyin al’umma domin tattauna matsalolin Nijeriya ko ma ba a kowani lokaci ba. Dole ya kasance sanne a wasu sassan kasar nan duk da yake ba wajibi ba ne hakan.
Ya kasance ya yi wa karamar hukumarsa hidima ko garinsa wanda ba za a ce ba a taba jin sunansa a kasar ba ko a bangaren aiki kamar irin su likita, dan jarida da sauransu, ya kamata ya kasance ya taba yin wani kokari na ciyar da al’umma