Daga Khalid Idris Doya, Bauchi
A ranar Lahadin da ta gaba ne da misalin karfe shida zuwa bakwai na yammaci wasu jerin manyan bishiyoyin madaci suka fado tun daga tushensu har kasa, Lamarin da ya yi mummunar barna ga jama’a, inda suka lalata gidaje da ma’aikatu da sauransu. Wakilinmu ya shaida mana cewa kimanin manyan bishiyoyi tara ne suka fadi a lokaci guda. Lamarin kuma ya auku ne sakamakon filfilawar iska mai karfin gaske a layin Bauci-Kolof dake tsakiyar garin Bauci.
Dakta Bala Musa Lukshi shi ne babban sakatare a ma’aikatar gona da albarkatun kasa na jihar, ya kuma bayyana cewa, faruwar lamarin ya biyo bayan babban iska ne da aka yi a layin, inda kuma ya ce bishiyoyin nan sun yi sama da shekara talatin ba tare da gyarasu ba. “A sakamakon haka ne wasu itatuwa suka karye inda suka rufe wannan hanyar baki daya sakamakon girman bishiyoyin da kuma yawan rassansu. Abun da ya jawo faduwar bishiyoyin dai shi ne kamar yadda muka lura su wadannan itatuwan an dasa su ne sama da shekara talatin, itatuwa ne da ake ce musu Madaci wanda yake yin girma sosai, a bisa girmansu da kuma rassa jijiyoyinsu suka gagara daukar bishiyar sakamakon yawa ne ya sanya iskan ya samu damar kayar da su har kasa a lokaci guda”. In ji Dakta Lukshi, Ya ci gaba da cewa nan take bayan samun labarin auwakuwar lamarin ma’aikatansu suka je suka hau sassare bishiyoyin domin kaudasu daga kan hanya, da kuma duba lafiyar sauran bishiyoyin.Inda ya ce, sun tabbatar yanzu haka akwai wasu bishiyoyin da suka fara lalacewa, inda ya ce, suna shirye -shiryen saresu domin kare lafiyar mutanen wannan yankin. A cewarsa, barin bishiyoyin haka nan babbar barazanace ga lafiyar jama’ar yankin.
Dangane da matakin shawo kan matsalar kuwa, Dakta Bala ya ce, sun rubuta inda suke neman izinin gwamnati domin su sare bishiyoyin gabaki daya domin canzasu da itatuwan da suka dace da wannan yanayin.A cewarsa yin haka ne kawai mafita. “Idan aka sauyasu da wasu itatuwan da ba su kai wannan girma ba, wadanda ba zasu zama barazana ga jama’a ba”. in ji sa
Duk kokarin da muka yi don jin ta bakin hukumar bayar da gajin gaggawa SEMA don samun bayani kan yanayin ta’asar da hasarar da bishiyoyin suka yi, hakan ya citura, kana da jin wani shiri da gwamnatin jihar ke yi na tallafa wa wadanda iftila’in ya fada musu, hakan kuma ya biyo bayan rashin samun mai rikon babban sakatare a ma’aikatar ne ya zuwa hada wannan rahoton.
Wakilin LEADERSHIP A YAU da ke Bauci ya lura da cewa, dukkanin bishiyoyin da suka fadin girmansu kusan daya ne da juna, inda mafiya yawa daga cikinsu sun yi matukar girma fiye da kima, a yayin da suka fadi suka bar madaidaita da kuma kananan bishiyoyin. Abun da muka sake lura da shi, shi ne kusan an shuka itatuwan ne a lokaci guda, a bisa haka ne suka fadi a tare.