Connect with us

RIGAR 'YANCI

Iyalin Shugaban Kwalejin Kimiyyar Lafiya Ta UNIZIK Na Zargin Rufa-rufa A Mutuwarsa

Published

on

Iyalin marigayi shugaban Kwalejin kimiyyar lafiya ta Jami’ar Nnamdi Azikiwe University da ke Nnewi a Jihar Anambra, Farfesa Onochie Udemezue, su na zargin wata rufa-rufa a al’amarin mutuwarsa.

Iyalin sun nuna fusatarsu ne a kan jinkirin da jami’ar ke yi na bayar da sakamakon gwajin da a ka ce an yi wa marigayi farfesan a kan annobar nan ta Korona.

An bayar da rahoton mutuwar Udemezue ne a ranar Alhamis bisa matsalar ciwon suga da kuma na annobar ta Korona. Amma a lokacin da iyalin na shi su ke yin wani jawabi a ranar Lahadi, sun ce kila za su bukaci yin gwajin daga wata kafar mai zaman kanta, domin sanin gaskiyar abinda ya kashe farfesan.

Mai magana da yawun iyalin, Orji Udemezue, ya ce “Mun yi bakin ciki da rade-radin da ake yadawa masu cewa dan’uwanmu kuma babanmu ya mutu ne a sakamakon kamuwa da cutar korona.

“Mu iyalinsa mu na da masaniya kwarai da gaske kan abin da a ke kira da cutar korona, mu na kuma sane da cewa akwai milyoyin mutane da suka kamu da cutar ta korona, sannan kuma dubunnai sun mutu a sakamakon kamuwa da cutar ta korona a fadin Duniyar nan, sannan mu na sane da cewa ba wai wani abin kunya ne ba a ce mutum ya kamu da Korona, ba kuma kamuwa da cutar yana alamta cewa mutuwa ta zo kenan ba.

“Mun kadu da ganin kwanaki uku sun shude a bayan mutuwar Farfesa Udemezue, amma har yanzun an gaza sakin sakamakon gwajin da aka ce an yi wa mamacin a kan cutar ta Korona ga iyalinsa. Wanda wannan abu ne da bai kamata ya wuce mintuna 15 ba a iya aiwatar da shi in dai komai kalau.

“Al’ummar kasa ya kamata su san cewa tun kafin mutuwar na shi, Farfesa Udemezue, ya nemi da a nuna masa sakamakon gwajin da aka ce an yi masa a kan cutar ta Korona, wanda kuma sam ba a nuna masa din ba. Hakan ya sanya mun fara tunanin akwai wani abin da ake nufin boyewa a kan maganar baki dayanta don haka mu na bukatar fayyacewa daga hukumomin na NAUTH.”

Da ya ke mayar da martani ta wayar tarho, babban Likitan Asibitin na NAUTH, Farfesa Anthony Igwegbe, cewa ya yi ba a saki sakamakon ne ba a hukumance daga hukumomin da su ka kamata, ya kara da cewa, sam babu wata rufa-rufa a cikin wannan maganar.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: