• English
  • Business News
Saturday, November 8, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Iyaye Mu Kara Himmar Samar Da Al’umma Mai Tarin Ilimi –Matar Gwamnan Katsina

by El-Zaharadeen Umar
2 years ago
Matar Gwamnan katsina

An gudanar da gasar adabi domin bunkasa ilimin ‘ya ‘ya mata karo na uku mai taken ‘Fatima Dikko Radda girls child education summit and literacy contest’.

Ita dai wannan gasa na da nufin karfafa gwiwar ‘ya ‘ya mata musamman abinda ya shafi karatun su tun daga matakin firamare har zuwa jami’a ta yadda za su rika samun wakilci a duk sauran al’amura.

  • Gwamna Radda Ya Yi Allah Wadai Da Hare-haren ‘Yan Fashin Daji A Jihar Katsina 
  • Yadda Mahara Suka Kashe Mutane Da Sace Wasu Da Dama A Wurin Maulidi A Katsina

A karo na uku na wannan gasa, an zakulo dalibai daga bangarori hudu da suka hada da karamar sikadara da babar sikadare da masu digiri da kuma masu digiri na biyu domin fafatawa a wannan gasa wanda kungiyar ‘read Right Multipurpose education society’ suka saba shiryawa.

Daliban da suka fafata acikin wannan gasa sun hada da dalibai 41 daga karamar sikandire da dalibai 54 daga babar sikandire sai dalibai 19 masu karatun digiri da kuma mutum biyu masu karatun digiri na biyu.

Daga cikin mahimman batutuwa da aka gudanar da wannan gasar ta bana sun hada da batun samar da tsaftattaccen ruwa sha da daidaito akan batun macce da Namiji da wakoki akan irin rawar da mata ke takawa wajan samar da tsaftattaccen ruwan sha da batun ciwon daji ‘cancer’ da dai sauransu
Haka kuma kowanne rikuni an fitar na daya zuwa na uku inda aka basu kyaututtuka da kudadai domin kara masu kwarin gwiwa musamman abinda ya shafi karatun su.

LABARAI MASU NASABA

Gwamna Dauda Lawal A Shekara 60: Inda Akwai Fata, Akwai Mafita

GORON JUMA’A

Da take gabatar da jawabi, uwargidan Gwamnan Jihar Katsina, Hajiya Fatima Dikko Umar Radda ta nuna farin cikinta a kan yadda dalibai suka nuna kwazo da jajircewa a lokacin wannan gasa da ta gudana.

Hajiya Fatima Dikko Radda na mai cewa hakika kun zama abin alfahari ga al’ummar Jihar Katsina ta yadda da irin haka ne za ku canza alkiblar ilimi musamman na ‘ya’ya mata a jihar Katsina da arewacin Nijeriya.

Ta kuma kara da cewa shirya irin wannan gasa zai kara wa sauran mata kwarin gwiwa domin su tashi tsaye wajan ganin an yi gogayya da wasu ta fannin ilimi da sauran bangarori.

“A yau nake kara tabbatarwa cewa ilimin ‘ya ‘ya mata abu ne da ke da matukar muhimmanci a rayuwar duniya da lahira saboda haka ina kara kira ga iyaye da malamai da masu ruwa da tsaki a kan sha’anin ilimi da mu kara ba da himma wajan samar da sabuwar al’umma mai dauke da tarin ilimi da zamani da na addini” in ji ta.

Tunda farko shugabar kungiyar ‘Read Right Multipurpose education society’ Aliyu Nasir Kankara ya bayyana wasu ayyukan wannan kungiyar inda ya ce an samu gagarumar nasara a cikin wannan shekarar ta 2023.

“Mun kaddamar da rabon littattafai a karamar hukumar Musawa da Dabai a karamar hukumar Danja, mun yi gangamin wayar da kai akan sha’anin shugabanci da kuma bayar da abinci a lokacin wata Ramadan din da ya gabata”. In ji shi.

Ya kara da cewa a shirin su na a koma makaranta ”Back to School Campaign’ sun samu nasarar dawowa da yaran da ba sa zuwa makaranta 7,500, sannan sun yi taron wayar da kai dangane da matsalar rikice-rikecen cikin gida da sauran batutuwa da suka shafi al’umma.

Ita ma a nata jawabin kwamishiniyar ilimi a matakin farko da babar sikandire Hajiya Hadiza Yar’adua ta yi bayanin cewa irin wannan gasa na nuna irin yadda aka nuna kulawa ga ilimin ‘ya ‘ya mata.

Ta ce ko ba komi an sanar da wata sabuwar hanya ta karfafa gwiwar ‘ya ‘ya mata wanda hakan ba zai sa a bar su a baya ba ta bangarori da dama.

” Yanzu muryoyin ‘ya ‘ya mata za su fara yin amo na gaskiya musamman abubuwan da suka shafi ilimi na zamani da kuma na addini” in ji ta.

Kazalika ita da take nata ta’aliki, kwamishiniyar harkokin mata ta jihar Katsina Hajiya Zainab Musa Musawa ta nuna mahimmancin yin ilimin ga ‘ya ‘ya mata musamman a wannan lokaci da ke da kalubale kala-kala na rayuwa.

Ta yi bayanin cewa ta ga mahimmancin yin ilimi wanda ta ce shi ne, tushe kuma ginshiki na kasancewarta a gaban wadannan dalibai tana yi masu jawabi, ta ce ba dan ilimi ba da sai dai wani abu ya hada su.

Bayan haka kwamishiniyar harkokin mata ta yi nuni cikin nishadi inda ta ce ” Bayan haka idan kuka duba mafiyawan matan da ke wannan baban tebur dukkan su ilimi ne ya kawo su wannan wuri.

An kammala wannan gasa ta adabi da bunkasa ilimi ‘ya ‘ya mata da aka kashe kwana biyu ana gudanarwa a Katsina tare da raba kyaututtuka ga wadanda suka samu nasara lashe gasar.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Gwamna Dauda Lawal A Shekara 60: Inda Akwai Fata, Akwai Mafita
Al'adu

Gwamna Dauda Lawal A Shekara 60: Inda Akwai Fata, Akwai Mafita

September 2, 2025
GORON JUMA’A
Goron Juma'a

GORON JUMA’A

August 15, 2025
GORON JUMA’A 8-8-2025
Goron Juma'a

GORON JUMA’A 8-8-2025

August 8, 2025
Next Post
Shigar Mutunci

Koya Wa Yara Shigar Mutunci (I)

LABARAI MASU NASABA

Shugaban Kasa Yana Bibiyar Zanga-zangar Matsin Rayuwa – Minista

Shirin Shugaba Tinubu Na ‘Renewed Hope’ Zai Karfafa Wa Manoma Gwiwa – Oyebanji

November 7, 2025
Shugabannin DSS Sun Gana A Kaduna, Sun Tattauna Matsalar Tsaron Arewa Maso Yamma

Shugabannin DSS Sun Gana A Kaduna, Sun Tattauna Matsalar Tsaron Arewa Maso Yamma

November 7, 2025
Cinikin Waje Na Kasar Sin Ya Karu Da Kashi 3.6 Cikin Dari A Watanni 10 Na Farkon Shekarar 2025

Cinikin Waje Na Kasar Sin Ya Karu Da Kashi 3.6 Cikin Dari A Watanni 10 Na Farkon Shekarar 2025

November 7, 2025
An Bukaci Manoma Su Rungumi Tsarin Noma Mai Jure Wa Sauyin Yanayi

An Bukaci Manoma Su Rungumi Tsarin Noma Mai Jure Wa Sauyin Yanayi

November 7, 2025
Kasar Sin Za Ta Dage Dakatar Da Shigo Da Waken Soya A Kan Kamfanonin Amurka Uku 

Kasar Sin Za Ta Dage Dakatar Da Shigo Da Waken Soya A Kan Kamfanonin Amurka Uku 

November 7, 2025
Abin Da APC Za Ta Yi Da Rinjayen Kashi Biyu Bisa Uku A Majalisar Tarayya

Abin Da APC Za Ta Yi Da Rinjayen Kashi Biyu Bisa Uku A Majalisar Tarayya

November 7, 2025
An Yi Kira Da A Zurfafa Hadin Gwiwa Tsakanin Sin Da Kasashen Afirka Don Bunkasa Masana’antu A Sassan Afirka

An Yi Kira Da A Zurfafa Hadin Gwiwa Tsakanin Sin Da Kasashen Afirka Don Bunkasa Masana’antu A Sassan Afirka

November 7, 2025
APC Da Uba Sani Ba Su Lashe Zaben Gwamnan Kaduna Ba -PDP

Yadda PDP Ta Yi Asarar Kudancin Kaduna

November 7, 2025
Kasar Sin Ta Musanta Zargin Da Wakilin Amurka Ya Yi Game Da Batun Sauyin Yanayi

Kasar Sin Ta Musanta Zargin Da Wakilin Amurka Ya Yi Game Da Batun Sauyin Yanayi

November 7, 2025
Mataimakin Firaministan Kasar Sin Ya Halarci Taron COP30 A Brazil

Mataimakin Firaministan Kasar Sin Ya Halarci Taron COP30 A Brazil

November 7, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.