A jiya Asabar 22 ga watan nan, jakadan kasar Sin a Amurka Xie Feng, ya amsa gayyatar halartar taro na 2 na tattaunawar sassan Sin da na Amurka game da batun tattalin arziki karkashin cibiyar Jimmy Carter, inda ya gabatar da jawabi ta kafar bidiyo.
A cikin jawabinsa, jakada Xie Feng ya ce ko kadan, hadin gwiwar Sin da Amurka bai taba zama na wani fanni ya ci riba dayan ya yi asara ba. Maimakon haka, kaso 41 bisa dari na kamfanonin Amurka dake kasar Sin na daukar Sin a matsayin kasa ta biyu a duniya, wajen samun ribar hada hadar kasuwanci.
- Dole Gwamnatin Tarayyar Nijeriya Ta Daina Barazana Ga Masu Sukar Ta – Amnesty
- An Kashe Askarawa 6 da ‘Yan Sa-kai 4 A Zamfara
Xie ya kara da cewa, matakin Amurka na mayar da batun kara haraji wani makami na neman biyan bukata, zai zamo tamkar “kaikayi da zai koma kan mashekiya”. Ya ce Sin a shirye take ta dauki matakai na warware damuwar juna ta hanyar tattaunawa da gudanar da shawarwari, bisa daidaito da martaba juna, amma maimakon haka Amurka na nacewa ga dorawa Sin laifi, tana kokarin dakile ta da nuna danniya, sai dai kuma a nata bangare, Sin za ta dauki dukkanin matakai da suka wajaba don kare hakkoki da moriyarta.
Daga nan sai Xie Feng ya jaddada cewa, wajibi ne Sin da Amurka su saba, su kuma ci karo da juna a wasu fannoni. Amma jigon daidaita hakan shi ne kaucewa keta hurumin moriyar juna, da kaucewa keta muradun juna. Ya ce goyon bayan “’yancin kan Taiwan” tsoma baki ne cikin harkokin gidan kasar Sin, kuma amincewa da “’yancin kan Taiwan” mataki ne na gurgunta zaman lafiya a zirin Taiwan. Yayin da kokarin amfani da batun yankin Taiwan wajen juya kasar Sin ba zai yi nasara ba, a daya hannun mataki ne mai matukar hadari. (Mai fassara: Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp