Jakadan kasar Sin dake Amurka Xie Feng, ya bayyana a kwanan baya cewa, sabon karfin samar da hajoji, da hidimomi masu karko, ba ma kawai ya shigar da sabon karfi, da ya inganta ci gaba mai inganci na Sin ba ne kadai, har ma ya zamo sabon karfi da ya inganta ci gaba mai dorewa tsakanin kasa da kasa.
Xie Feng ya bayyana hakan ne a ranar Jumma’a, yayin da yake zantawa da mujallar “Newsweek” ta Amurka. Ya ce sabon karfin samar da hajoji da hidimomi masu karko, a takaice na nufin inganta karfin samarwa na zamani, da kuma samun ci gaba mai inganci ta hanyar yin kirkire-kirkire, da zurfafa gyare-gyare.
- Sojojin Sin Da Amurka Sun Gana A Hawaii Don Tattauna Batun Tsaron Teku Da Na Sararin Sama
- Jiragen Kasan Nijeriya Sun Tara Kudin Shiga Naira Biliyan 1 A Cikin Wata Uku – NBS
Ya bayyana cewa, habaka bude kofa ga waje bisa babban mataki, ita ce ma’anar bunkasa sabon karfin samar da hajoji da hidimomi masu karko. Kaza lika bude kofa ga waje bisa babban mataki, hanya ce ta wajibi ga Sin wajen samun ci gaba, wadda ke haifar da tarin riba ga ci gaban kasa da kasa. Har ila yau, ci gaba da habaka babbar kasuwa, shi ne tushen ci gaban tattalin arzikin Sin, kuma damammakin tarihi ne na kasashen duniya, a fannin samar da nasara ta hanyar hadin gwiwa.
Kaza lika, Xie Feng ya ce, tare da kasancewar sabon karfin samar da hajoji da hidimomi masu karko a Sin, da kuma manufofi masu amfani da ake fitarwa a kai a kai, wasu masu kula da kamfanoni na Amurka, da sauran kasashen duniya, sun riga sun tarar da wadannan dammamakin tarihi masu daraja, suna kuma shirya gudanar da ayyukansu.
Ya jadadda cewa, ya kamata bude kofa ga kasashen waje ya kawo alherai ga juna, kuma yayin da Sin ke maraba da bude kofa ga kasashen duniya, ya kamata sauran kasashen duniya ma su yi hakan. (Safiyah Ma)