Jakadun kasashe 25 da suka hada da Dominica da Myama da Iran sun ziyarci birnin Urumqi da yankin Kashgar da birnin Aksu na jihar Xinjiang ta kasar Sin tsakanin ranakun 31 ga watan Yuli zuwa ranar 4 ga wannan wata, bisa gayyatar da ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ta yi musu, inda suka yi musaya mai zurfi da mazauna biranen ‘yan kabilu daban daban, tare kuma da ganin ci gaban tattalin arziki da zaman takewar al’umma dake Xinjiang da idannunsu kai tsaye.
Yawancin jakadun sun bayyana cewa, akwai jituwa a zaman takewar al’ummar Xinjiang, tattalin arzikin jihar yana samun ci gaba cikin sauri, al’adun jihar su ma suna samun wadata yadda ya kamata. A bayyane ake ganin cewa, al’ummar Xinjiang na jin dadin rayuwarsu, jita-jitar da wasu kafafen watsa labarai na kasashen yamma suke bazawa ba su dace da ainihin hakikanin yanayin da Xinjiang ke ciki ba.
A cikin ‘yan shekarun da suka gabata, gwamnatin jihar Xinjiang ta yi kokari matuka domin yaki da ta’addanci bisa doka, kuma ta samu sakamako a bayyane. (Mai fassara: Jamila)