Hukumar shirya jarabawar shiga jami’o’i ta kasa (JAMB) ta sanya maki 140 a matsayin mafi karancin maki na shekarar 2024 da za a iya shiga jami’o’in kasar nan.
Shugaban hukumar, Farfesa Ishaq Oloyede ne ya bayyana hakan a yayin tattaunawa da masu ruwa da tsaki kan bayar da takardar shiga manyan makarantu a shekarar 2024.
- Malamin Tsangaya Ya Shiga Hannu Kan Zargin Luwadi Da Ɗalibai A Jigawa
- Da Ɗumi-ɗumi: Gwamnatin Tarayya Da Ƙungiyoyin Ƙwadago Sun Amince A Kan N70,000 Mafi Ƙarancin Albashi
Oloyede ya ce, an amince da 100 a matsayin mafi karancin maki a Kwalejin Kimiyya da Kwalejojin Ilimi.
Farfesa Ishaq ya bayyana cewa, wadannan mafi karancin maki da aka bayyana, su ne mafi ƙanƙantar maki, amma hakan ba yana nufin dole ne hukumomin manyan makarantu su bi tsarin.