Hukumar shirya jarrabawar shiga makarantun gaba da sakandire (JAMB), ta fitar da karin sakamakon jarabawar gama gari ta (UTME) 36,540, wanda tunda farko ta rike don yin bincike akansu.
Hukumar a cikin wata sanarwa da ta fitar ta hannun mai magana da yawunta, Dr. Fabian Benjamin, ta ce, sabbin sakamakon sun hada da 531 da aka fitar a makon da ya gabata, wanda ya kawo adadin zuwa 1,879,437.
- JAMB Ta Fitar Da Sakamakon Jarrabawar 2024, Sakamako 64,624 Na Karkashin Bincike
- Magudin Jarrabawar UTME: Okebukola Ya Shawarci Makarantu Da Su Rungumi Tsarin JAMB
Hukumar ta yi gargadi kan wata wasika ta bogi da wani dan damfara ya shirya kuma aka yada ta a kafafen sada zumunta na yanar gizo da ke cewa ta fito ne daga hukumar, inda ta ke nuni da cewa, sakamakon gwarazan dalibai na UTME na 2024, yana hannun kwararru masana na’u’ra don tantance ingancin sakamakon. Takardar bogin ta kara da cewa, ana kyautata tsammanin kutse ga rumbun tattara sakamakon Hukumar JAMB, don haka, ana tunanin sake shirya jarrabawar.
Hukumar ta sake nanata cewa, sakamakon UTME na shekarar 2024 da sauran shekarun da suka gabata suna nan a killace, cikin ajiyar na’ura adana bayanai ta yanar gizo inda wani ba zai iya yin kutse ba.