Abba Ibrahim Wada" />

James Rodriguez Zai Zabi Everton A Kan Arsenal

Wasu rahotanni daga kasar Ingila sun bayyana cewa dan wasan gaban kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid, James Rodriguez, zai zabi komawa kungiyar kwallon kafa ta Eberton akan Arsenala kakar wasa mai zuwa kamar yadda rahotanni suka bayyana.

 

A satin daya gabata ne dan wasan gaban na Real Madrid, ya bayyana burinsa na ganin ya koma kasar Ingila domin ci gaba da buga gasar firimiya a kakar wasa mai zuwa bayan da kungiyoyi da dama a gasar suke zawarcinsa.

 

Dan wasan mai shekara 28 a duniya ya koma Real Madrid ne a shekara ta 2014 kuma tun bayan komawarsa kungiyar ya fara samun matsala da masu koyar da kungiyar a baya sai dai a shekara ta 2021 kwantiraginsa zai kare da kungiyar.

 

Kungiyoyin Arsenal da Eberton ne dai suke zawarcin dan wasan gaban dan kasar Colombia wanda kungiyoyi da dama a kasar Italy ciki har da Napoli suke zawarci kuma ana ganin a kakar wasa mai zuwa zai yanke hukuncin inda zai koma.

 

Yawan zuwa ciwo shine yasa har yanzu dan wasan wasanni bakwai ya bugawa Real Madrid a wannan kakar da ake bugawa duk da cewa daman dai baya cikin tsarin Zidane na ‘yan wasan da yake son yin amfani dasu.

 

Itama kungiyar kwallon kafa ta Eberton tana daya daga cikin kungiyoyin da suke zawarcin dan wasan bayan da sukayi aiki tare da kociyan kungiyar, Carlo Ancelotti, wanda ya koma kungiyar a watan Janairun wannan shekarar kuma James yana ganin zaifi samun damar buga wasanni akai-akai a gasar Firimiya.

 

Exit mobile version