Hukumar Karota ta Jihar Kano ta yi nasarar cafke wata tirela makare da giya, a kan titin Bello Dandago da ke kwaryar birnin Kano.
Jami’an KAROTA sun kama motar ne da misalin karfe 2:30 na daren jiya Laraba, a kokarinsu na shiga cikin Sabon Gari a Kano.
- An Kashe ‘Yan Boko Haram 49 A Sansaninsu 3 Yayin Luguden Wuta Ta Sama
- Ambaliya: An Tsinto Gawarwakin Mutum 15 A Kogin Maiduguri
Jami’an Hukumar ne suka samu nasarar cafke motar a lokacin da suka bukaci direban motar ya gabatar musu da takardar shaidar abin da ya dauko ta ‘Way Bill’ inda ya bayyana musu cewa Kwali ya dauko.
Bayan da jami’an suka matsa bincike sai suka tabbatar da Giya ce a cikin babbar motar.
Shugaban KAROTA, Baffa Babba Dan’Agundi, ya bayyana cewa ba za su gaji ba wajen kama duk wani nau’in kayan da aka ci garo da su, wanda dokar Jihar Kano ba ta amince a shigo da su ba.
Ya kara da cewa za a kara baza jami’an KAROTA musamman kan manyan titinan jihar, domin ganin an dakile shigowar kayayyakin da dokar Jihar Kano ta haramta.
kasa da mako guda hukumar ta cafke manyan motocin tirela makare da giya wadanda adadinta ya kai fiye da Kwalba dubu arba’in (40) da kudinta ya haura Naira miliyan 40.
Da zarar an kammala bincike za a mika giyar ga hukumar Hisbah ta Jihar Kano domin daukar mataki na gaba.