Jami’an tsaron hadin guiwar sojoji, ‘yansanda, mafarauta da ‘yan banga sun samu nasarar ceto mutane 29 daga hannun masu garkuwa da mutane a gundumar Lere da ke karamar hukumar Tafawa Balewa a jihar Bauchi kwanakin baya.Â
Gwamnan jihar Bauchi, Bala Muhammad, shi ne ya sanar da hakan dangane da nasarori da ayyukan jami’an tsaro a gundumar Lere ranar Litinin yayin wata ziyarar mara baya da ya kai wa jami’an tsaron, ya kara da cewa, ‘yan fashin daji su 67 ne suka sheka lahira sakamakon tunkararsu da jami’an tsaro a karkashin ‘yansandan jihar suka yi.
- An Kama Masu Laifi 537, An Daure 250 Cikin Wata 3 A Borno
- Gwamnatin Tarayya Za Ta Dauki Matasa Miliyan 5 Aiki A Sabon Shirin N-Power – Minista
Domin bayar da dama wajen saukaka ayyukan fatattakar masu garkuwa da mutane, gwamnan ya gargadi dukkanin wani basaraken da aka samu da mara baya ko sako-sako wa ‘yan fashin daji a masarautarsa to lallai za a dauki matakin ladabtarwa a kansa.
A cewarsa, sarakunan da suke mara baya wa masu garkuwa da mutane suna da hadari matuka a cikin al’umma fiye ma da ‘yan bindigan.
Gwamna Bala ya sanar da shirin gwamnatin jihar na daukan jami’an tsaron sa-kai na cikin gida su sama da 20,000 wadanda za su samu horo na musamman daga wajen hukumomin tsaro domin kara karfi wajen yaki da masu garkuwa da mutane da sauran matsalolin tsaro a fadin jihar Bauchi.
Abdulkadir Muhammad ya nuna muhimmancin aikin hadin guiwa a tsakanin ‘yan banga, mafarauta, sarakuna da hukumomin tsaro wajen yaki da ‘yan ta’adda da ayyukan ta’addancin a fadin jihar.
A wani mataki na qarfafa guiwar jami’an tsaron sa-kai, gwamnan ya bayar da kyautar naira miliyan goma (10m) wa farauta da ‘yan banga su 200 da suka shiga aka dama da su wajen ceto mutanen da aka yi garkuwa da su.
Bugu da kari, ya kuma bayar da kyautar Babura kirar Bajaj domin karfafa musu guiwa wajen cigaba da ayyukan yaki da bata-gari, ya ce za su kara samar musu da mashinan sintiri kwanan nan.
Daga nan sai gwamnan ya yaba wa kokarin hadakar jami’an tsaron wajen cimma wannan nasarar da ma sauran nasarorin da suke samu a kan ‘yan fashin daji, ya ba su tabbacin cigaba da mara musu baya da tallafa musu da kayan aiki da kudade domin samun nasara wajen kare rayuka da dukiyar al’umman jihar.
Tun da farko, kwamishinan ‘yansandan jihar Bauchi, CP Musa Muhammed Auwal, ya nuna farin cikinsa bisa yadda ake samun aikin hadin guiwa a tsakanin hukumomin tsaron wajen yaki da matsalolin tsaro a fadin jihar.
Ya bada tabbacin hadin guiwarsu ga gwamnatin jihar da masu ruwa da tsaki hadi da al’umman jihar domin cigaba da kyautata harkokin zaman lafiya da kwanciyar hankalin al’umman jihar baki daya.
Shugaban riko na karamar hukumar Tafawa Balewa da Hakimin Lere Sama’ila Wakili da Suleiman Mohammed bi da bi sun jinjina wa gwamna Bala bisa damuwa da yake yi kan kan tsaro da tabbatar da kare rayuka da dukiyar al’umman jihar baki daya.