Hukumar gudanarwar Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Aliko Dangote da ke Wudil (ADUSTECH) ta ce ba ta daukar ma’aikata, sabanin yadda kafafen sada zumunta ke yada cewa suna shirin daukar ma’aikata.
Malam Abdullahi Datti, mataimakin magatakardar yada labarai na ADUSTECH ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a Kano ranar Litinin.
- Gwamnatin Kano Ta Nada Jega A Matsayin Shugaban Jami’ar Sa’adatu Rimi
- BUK Ta Karrama Farfesa Rasheed Bayan Ya Shafe Shekaru 7 A Hukumar NUC Ta Kasa
“Mahukuntan jami’ar na sun bayyana a fili cewa labarin karya ne kuma ba shi da tushe, don haka ya kamata jama’a su yi watsi da shi,” in ji Datti.
Ya kuma yi kira ga jama’a da su daina yada irin wannan jita-jita da bata da tushe bare makama.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp