Jami’ar Ibadan ta karama wadanda suke da niyyar samun ilimin jami’a a fadin tarayyar Nijeriya,da suka kasa samu ta JAMB cewar yanzu dama ta zo domin kuwa suna iya karatun a jami’ar Ibadan UI.
Makarantar ta yi kira da wadanda suka cancanta da su yi amfani da damar da ta samu ta Jami’ar na karatu daga gida kuma ta kafar sadarwa ta zamani daga shekarar karatu ta shekara mai zuwa.
- Nazari Kan Yadda Za A Iya Samun Wadatacciyar Riba A Kiwon Jimina
- ADC Ta Umarci Dukkan Mambobinta Su Yi Murabus Daga Tsoffin Jam’iyyunsu
Jami’ar ta bayyana cewa ta bude wurin tantancewa na musamman ga duk wadanda suka rubuta jarrabawa cancancewa ta Post UTME suka muma sha’awarsu ta yin karatun daga gida tsarin na jami’ar.
Darektan sashen , Farfesa Babatunde Omobowale, ya ce matakin da aka dauka wata babbar dama ce ga daliban da suka cancanta a fadin tarayyar Nijeriya, wdanda basu samu damar karatu ba ta JAMB ko kuma basu samu damar karatun ba, a irin jami’a mai farin jini irin Jami’ar Ibadan.
Ya ce, “Ana bukatar dalibai su daidaita bayanansu kamar yadda ya dace. Ya ce bayan sun yi hakan ne, sai daliban su zabi abinda ya dace wanda ya shafi neman damar karatum ko kuma su je ofishin bada damar karatu na Jami’ar da yake kan hanyar Sasa -Ajibode, saboda tantancesu.
“Ba wani bata lokaci bane za’a fara harkar. Idan ka cancanta amma har yanzu baka nemi a baka dama ba, zaka iya neman a baka damar yin hakan. Sai ka nemi damar hakan ta https:// modeofstudy.ui.edu.ng domin ka samu digirin da yake da muhimmanci na jami’ar Ibadan.Irin tsarin karatu na UI-ODeL yana bada dama yadda za a samu koya ta fasaha da kwarewa mai amfani.
“Wadanda suke da sha’awar yin karatun akwai bukatar ya samu nasara kan darussan daya rubuta jarrabawa biyar, a zama daya, ko kuma shida a rubuta jarrabawa sau biyu.”
Omobowale ya kara jaddada cewar sababbi da kuma dalibai masu shiga makarantar an kaddamar da su a wurin da ake rubutar jarrabawar CBT Compled, bayan haka za su san yadda lamurran da tsare- tsaren karatun suke, da kuma irin taimakon da ake baiwa dalibai.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp