ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Sunday, December 21, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Jami’ar MAAUN Ta Rantsar Da Sabbin Dalibai Sama Da 500 A Kano

by Khalid Idris Doya
3 years ago
MAAUN

Jami’ar Maryam Abacha ta Nijeriya (MAAUN) da ke jihar Kano a ranar Litinini ta rantsar da sabbin dalibai sama da 500 da suka samu gurbin karatu na shekarar 2021/2022.

Kididdiga ta nuna cewa MAAUN Kano ita ce jami’a mai zaman kanta daya tilo daga cikin jami’o’i masu zaman kansu guda 111 da ake da su a Nijeriya da suka fara ayyukan karatu da dalibai kusan dubu daya a lokaci guda.

  • Shin Zargin Kasar Sin Ya Fi Yaki Da Ta’Addanci Muhimmanci?
  • Harin Kuje: DSS Ta Fitar Da Rahoton Tsaro 44 Kafin Kai Harin – Wase

A jawabinsa, shugaban Jami’ar MAAUN Kano, Farfesa Mohammad Israr, ya ce daliban da suka samu gurbin karatu a jami’ar a hukumance sun shiga shirin karatu bisa amincewar hukumar kula da jami’o’i ta kasa (NUC).

ADVERTISEMENT

“Cikin farin ciki nake yi wa daukacin dalibai barka da zuwa jami’ar, na yi imani cewa Allah zai yi amfani da wannan jami’a wajen bunkasarku da ci gabanku ta kowane fanni na rayuwa.

“Ina taya iyayenku murna kan babban rawar da suke takawa a rayuwarku, ina addu’ar ka da wannan kokarin nasu ya tafi a banza,” in ji Shugaban MAAUN.

LABARAI MASU NASABA

An Sako Ragowar Ɗalibai Da Malamai Da Aka Sace A Makarantar Katolika Ta Neja

Akpabio, Ganduje, Ogundoyin Sun Halarci Naɗa Seyi Tinubu Sarauta

Shugaban ya ce Jami’ar tana koyar kwasa-kwasai da ke da kimar kasuwanci ga dalibai yana mai jaddada cewa tsarin koyarwa a jami’ar ya shafi harkokin kasuwanci da kuma dogaro da kai.

“Saboda haka wadanda suka kammala karatu a wannan jami’a ba za su shiga jerin masu neman aikin yi ido rufe ba a kasar nan, za su kasance wadanda suka assasa da kuma shiga sahun gaba a harkokin kasuwanci nan da wasu shekaru masu zuwa,” in ji Farfesa Isar.

A cewarsa, MAAUN Kano jami’a ce da ta shafi dalibai domin wuri ne da zai iya gyara shugabannin da za su zo a gaba.

“Muna alfahari da horar da dalibai a ayyukan ilimi. Muna mai da hankali kan habaka halayen dalibanmu bisa tsammanin cewa idan sun kammala karatun, za su ba da gudummawa mai ma’ana ga bayanan ci gaba a duk fadin duniya,” in ji shi.

Shugaban, wanda ya taya sabbin daliban murna da samun gurbin shiga bayan sun samu tantancewa da gwaje-gwajen jarabawa, ya shawarce su da su yi koyi da malamansu ta hanyar nuna tarbiya da sauke nauyin da ya rataya a wuyansu.

Ya kuma gargadi daliban da aka rantsar da su bi ka’idojin Jami’ar da kuma zama masu kyawawan halaye tare da sanya tufafi na mutunci.

A nata jawabin, kwamishiniyar ilimi ta jihar Kano, Dakta Mariya Bunkure, ta shawarci daliban da aka rantsar da su maida hankali wajen karatunsu, duba da irin makudan kudaden da iyayensu suka biya domin yin karatu a jami’ar.

Bunkure, wanda kuma memba ce a hukumar gudanarwar Jami’ar, ta gargadi daliban da su guji yin wani abu da zai iya bata sunan su da na jami’ar.

Ta yaba wa wanda ya kafa jami’ar, Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo, bisa kafa jami’ar wadda ta kasance daya daga cikin mafi inganci a kasar nan.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

An Sako Ragowar Ɗalibai Da Malamai Da Aka Sace A Makarantar Katolika Ta Neja
Manyan Labarai

An Sako Ragowar Ɗalibai Da Malamai Da Aka Sace A Makarantar Katolika Ta Neja

December 21, 2025
Akpabio, Ganduje, Ogundoyin Sun Halarci Naɗa Seyi Tinubu Sarauta
Manyan Labarai

Akpabio, Ganduje, Ogundoyin Sun Halarci Naɗa Seyi Tinubu Sarauta

December 21, 2025
Tashar Teku Ta Ciniki Mai ‘Yanci Ta Hainan Ta Bude Sabon Babin Hadin Gwiwar Sin Da Kasashen Afirka
Ra'ayi Riga

Tashar Teku Ta Ciniki Mai ‘Yanci Ta Hainan Ta Bude Sabon Babin Hadin Gwiwar Sin Da Kasashen Afirka

December 21, 2025
Next Post
Sojoji Sun Sake Ceto ‘Yan Matan Makarantar Chibok 2

Sojoji Sun Sake Ceto ‘Yan Matan Makarantar Chibok 2

LABARAI MASU NASABA

An Sako Ragowar Ɗalibai Da Malamai Da Aka Sace A Makarantar Katolika Ta Neja

An Sako Ragowar Ɗalibai Da Malamai Da Aka Sace A Makarantar Katolika Ta Neja

December 21, 2025
Raphinha Da Yamal Sun Ci Ƙwallaye Yayin Da Barcelona Ta Doke Villarreal

Raphinha Da Yamal Sun Ci Ƙwallaye Yayin Da Barcelona Ta Doke Villarreal

December 21, 2025
Davido Zai Raƙashe A Bikin Buɗe Gasar AFCON 2025 A Morocco

Davido Zai Raƙashe A Bikin Buɗe Gasar AFCON 2025 A Morocco

December 21, 2025
Yankin Rijiyoyin Mai Na Teku Mafi Girma Na Kasar Sin Ya Ba Da Rahoton Yawan Mai Da Iskar Gas Da Ya Fitar A Shekara

Yankin Rijiyoyin Mai Na Teku Mafi Girma Na Kasar Sin Ya Ba Da Rahoton Yawan Mai Da Iskar Gas Da Ya Fitar A Shekara

December 21, 2025
An Bukaci Bunkasa Fannin Kiwo A Hadin Gwiwar Sin Da Afirka

An Bukaci Bunkasa Fannin Kiwo A Hadin Gwiwar Sin Da Afirka

December 21, 2025
Akpabio, Ganduje, Ogundoyin Sun Halarci Naɗa Seyi Tinubu Sarauta

Akpabio, Ganduje, Ogundoyin Sun Halarci Naɗa Seyi Tinubu Sarauta

December 21, 2025
Tashar Teku Ta Ciniki Mai ‘Yanci Ta Hainan Ta Bude Sabon Babin Hadin Gwiwar Sin Da Kasashen Afirka

Tashar Teku Ta Ciniki Mai ‘Yanci Ta Hainan Ta Bude Sabon Babin Hadin Gwiwar Sin Da Kasashen Afirka

December 21, 2025
Tinubu

Dambarwar Naɗa Muƙamai Da Soke Su A Gwamnatin Tinubu

December 21, 2025
Zaben Fidda Gwani A APC: Sanatocin Jigawa Sun Rasa Tikitin Komawa Majalisa

APC Za Ta Gudanar Da Babban Taronta Na Kasa A Watan Maris

December 21, 2025
Mun Shirya Tsaf Domin Lashe Gasar AFCON Ta Bana – Bassey

Mun Shirya Tsaf Domin Lashe Gasar AFCON Ta Bana – Bassey

December 21, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.