Hukumar gudanarwan Jami’ar Umaru Musa Yar’adua dake Katsina ta amince da maki 170 na hukumar share fagen shiga jami’a wato JAMB a matsayin makin da zai ba da damar shigar jami’a a zangon karatu na shekara ta 2017/208.
An dauki matakin ne a lokacin taronta da take yi a kai a kai karo na 85 dake a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun jami’in hulda da jama’a ta jihar Fatima Sada Kaita.
Sanarwar ta kara da cewa, ya zuwa yanzu, dalibai sama da dubu goma sha biyar suka zabi jami’ar ta Umaru Musa Yar’adua a matsayin zabinsu. Sai dai sanarwar ta bayyana cewa hukumar kula da jami’o’i ta kasa ta amince jami’ar ta Umaru Musa Yar’adua cewa dalibai dubu biyu da dari biyar da saba’in da bakwai zasu zauna jarrabawar harda wadanda zasu zauna jarabawar kai tsaye.
Kamar yadda sanarwar ta ce jami’ar ta yanke shawarar cewa za a gudanar da jarrabawar ga dukkanin wadanda suka zauna jarrabawar suka samu maki 170 ko sama da haka na JAMB din a ranar 26 da 27 ga watan Satumba shekarar nan da muke ciki.