Jam’iyyar APC Ta Tsayar Da Dan Tarauni Takarar Shugabancin Karamar Hukumar Madobi

Daga Usman Suleiman Sarki Madobi

Ginshikin siyaya shi ne samar da shugabanci musamman a karamar hukuma wadda ta fi kusa da jama’a.

A bisa doron haka aka samar da dimokradiyya domin samar da shugabanci a matakai daban-daban ciki har da kananan hukumomi wanda sune mafi kusa da talaka. Sanin kowa ne cewa kundin tsarin mulkin kasa ya fayyace cewar sai mutumin da ya zama dan asalin yanki shi ne yake da damar tsayawa zabe don shugabantar al’ummar yankinsa, amma a yau abin ba haka yake ba a karamar hukumar madobi, domin Jamiyyar APC ta tsayar da dan asalin karamar hukumar Tarauni a matsayin dan takarar shugabancin karamar hukumar Madobi.

Wannan kuwa duk da tarin ‘yan takarar da suka fito daga karamar hukumar wanda hakan ya saba da tanadin kundin tsarin mulkin kasa.

Ba abin da ya fi a mulkin Dimokradiyya ga al’ummar kananan hukumomi musamman na karkara fiye da su samu Dansu kuma mai kishin su ya zama shugaban su domin wannan zai bashi dama ya zage ya yi aiki domin kawo wa jama’arsa ayyukan ci gaba tare da raya kasa, wadanda aiwatar dasu zai inganta rayuwar jama’a tare da kawo ci gaba mai amfani da yaduwar arziki.

Muhimmacin wannan a cikin al’umma shi ke sanya wa shugabanni na kananan hukumomi sabo da  kusancin su da jama’a. Sukan yi kokari wajen sauke wannan nauyi domin basu da makoma sai cikin al’ummarsu, wanda rashin yin hakan ba abin da zai biyo bayan hakan sai da nasani.

A irin wannan yanayi, ba abin da ya fi face a bai wa jama’a dama domin su duba, tare da fitar da wanda zai shugabance su, daga cikin ‘ya’yansu ‘yan asali wadanda basu da wani buri fiye da kawo ci gaba a yankinsu kuma suna tare da jama’arsu ko da zabe ko ba zabe, alakarsu na nan mai kyau tsakaninsu da jama’arsu, amma sai ga shi a wannan kakar zabe mu ’yan karamar hukumar Madobi an yi mana karfa-karfa an kakaba mana Alhaji Lawan Yahaya Tarauni a matsiyin dan takarar shugabanci karamar hukuma wanda a baya yayi kokarin tsayawa takarar wakilcin karamar hukumar a  majalisar dokoki ta jiha, amma ba a bashi dama ba saboda bashi da alaka da al’ummarmu.

Duk da masu ikirarin cewa Alhaji Lawan Yahaya  dan Daburau ne gidan Yahaya Abdulkadir amma abin mamaki a duk garin Daburau babu koda gidan su na gado ba ballantan gonar gado ko a ce ga danginsa.

Mu dai kam mu san ba a sake wa tuwo suna kuma baza mu amince da wannan cushe ba domin wannan ba abu ne na ka’ida ba face tauye mana hakki a matsayinmu na yan karamar hukumar Madobi.

A karshe nake kira ga mahukunta musamman mai girma Gwamnan Jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje wanda a gabansa aka aiwatar da wannan hukunci na tsayar da Dan Tarauni a matasayin dan takara a Madobi da ya duba wannan al’amari don tabbatar da adalci ga al’ummar karamar hukumar Madobi.

 

Exit mobile version