Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya ce jam’iyyar Labour Party, ba za ta tabuka abun arziki ba tunda dan takararta na shugaban kasa, Peter Obi, ya ki amincewa ya zama abokin takararsa a zaben 2023.
Kwankwaso ya bayyana haka ne a ranar Asabar ga manema labarai bayan kaddamar da ofishin jam’iyyar NNPP a jihar Gombe.
- ‘Yan Sanda Sun Kame Karin Mutum 7 ‘Yan Kungiyar Asiri A Edo
- An Umarci Sarakunan Gargajiya A Katsina Da Su Tabbatar Da Jama’arsu Sun Yi Rajistar Zabe
Dan takarar shugaban kasar, ya ce idan ya zama abokin takarar Obi to jam’iyyar NNPP za ta durkushe.
A cewarsa, yankin kudu maso gabas zai rasa wata babbar dama mai kyau idan dan takarar jam’iyyar LP bai zama abokin takararsa ba a 2023.
“Daga tattaunawar da aka yi da jam’iyyar Labour, babban batu shi ne wanda zai zama shugaban kasa idan jam’iyyun suka hade.”
“A karshen ranar, wasu daga cikin wakilanmu sun yi tunanin cewa ya kamata a samar da ma’auni dangane da shekaru, cancanta, gogewar aiki da sauransu.
“Tabbas daya bangaren ba zai so hakan ba. Galibin mutanen da suka fito sun yi imanin cewa dole ne fadar shugaban kasa ta je can. Idan na yanke shawarar zama mataimakin shugaban kasa ga wani; NNPP za ta ruguje, domin jam’iyyar ta dogara ne a kan abin da muka gina a cikin shekaru 30 da suka wuce.
“Na yi shekara 17 a matsayin ma’aikacin gwamnati; muna magana ne game da shekaru 47 na aiki wanda ke da wuya a rike NNPP a yanzu.
“Ko abokina (Peter Obi) yana son ya karbi takarar mataimakin shugaban kasa, wasu mutanen yankin kudu maso gabas ba za su yarda ba, wanda hakan babbar asara ce a gare su.
“Wannan babbar dama ce, idan suka rasa ta, za su yi dana sani a gaba.”