Daga Isah Ahmed
Wakilai masu zabe, na ‘yayan jam’iyyar PDP, daga mazabu 11 na Karamar Hukumar Lere, da ke jihar Kaduna, sun gudanar da zaben sababbin shugabannin da zasu ja ragamar shugabancin jam’iyyar, a karamar hukumar a garin Saminaka, a karshen makon da ya gabata.
Sababbin shugabannin da aka zaba, sun hada da Muhammad Lawal Aliyu a matsayin Shugaba, da Jafaru Waziri Mataimakin shugaba da Musa Chitta Sakatare da Surajo Sani Mataimakin sakatare da Dogara Hakuri Shugaban matasa da Iyami Adamu Shugabar Mata da Ahmed Hamza Jami’in watsa labarai da Ummar Abdu Mataimakin jami’in watsa labarai da Abdulwahab Sulaiman Sakataren tsare tsare da Turaki Shawara Sakataren kudi da Hayatu Ibrahim mai binciken kudi da Dauda S. Umar Ma’ajiyi da Bello Jafaru Mai bayar da shawara kan harkokin shari’a.
Da ya ke jawabi bayan kammala zaben, Mataimakin shugaban jam’iyyar PDP na jihar Kaduna, Alhaji Ibrahim Lawal Nuhu Kayarda ya taya sababbin shugabannin, murnar nasarar da suka samu.
Ya yi fatar wannan nasara zata kawo wa jam’iyyar nasara, a karamar hukumar a zabubbuka masu zuwa.
Ya yi kira ga al’ummar karamar su zauna lafiya, kuma su cigaba da zamantakewa kamar yadda a ka saba.
Shi ma a nasa jawabin, Dan majalisar wakilai ta ta tarayya Mai wakiltar mazabar Lere, Alhaji Muhammad Lawal Rabi’u ya yi kira ga shugabannin da aka zaba, su rungumi kowa da kowa.
“Dole ne ku tsaya ku ga yadda zaku hada kan ‘yayan wannan jam’iyya, a karamar hukumar Lere. Domin jam’iyyar ta sami nasara a dukkan zabubbukan da za a gudanar nan gaba.Kuma ina kira ga dukkan magoya bayan jam’iyyar PDP na Najeriya, mu hada kai mu yi hakuri da juna. Domin sai mun hada kai, mun yi hakuri da juna, sanna ne zamu sami nasarar karbar, gwamnatin kasar nan.”
A nasa jawabin, Sabon Shugaban jam’iyyar ta PDP na Karamar Hukumar ta Lere, Muhammad Lawal Aliyu Saminaka ya yi godiyz ga Allah, kan wannan nasara da ya samu, kuma ya yi godiya ga dukkan wadanda suka bada gudunmawa, wajen ganin an sami wannan nasara.
Ya yi kira ga wadanda suka yi takara, su zo su hada kai domin su sami nasara a wannan jam’iyya, a dukkan zabubbuka masu zuwa.