Kungiyar Jam’iyyatu Ansaariddeen Attajjaniyya (JAMAAT) ta yi hadin gwiwa da kungiyoyin kasashen waje domin ciyar da al’ummar Nijeriya dama na duniya baki daya gaba.
Kungiyar JAMAAT ta gudanar da taron hadin gwiwar ne shalkwatanta da ke 4th Abenue a Gwarinpa cikin garin Abuja, wanda ya sama halartar manyan baki ciki da wajen Nijeriya,
Da yake jawabi a wurin taron hadin gwiwar, Babban Sakataren Kungiyar JAMAAT na kasa, Alhaji Alkasim Yahaya ya bayyana cewa an gudanar da wannan taron hadin gwiwa ne domin lalubo hanyar da za a hada hannu da karfe wajen ciyar da al’ummar kasar nan gaba.
Ya kara da cewa ya tabbatar da cewa hadin gwiwar kungiyoyin zai samar da gagarimin sauyi ga kasar nan dama al’ummar Afirka da kuma na duniya baki daya.
Ya ce, “Tabbas na san cewa a duk lokacin da ake kokarin hadin kai, to dole ne a bukaci gina gaskiya a tsakanin juna. Tarihi ya nuna cewa akwai masu bukatar shigowa kasar nan domin zuba jari ko kuma bayar da taimako, amma daga kasarshe sakamakon rashin gaskiya sai abun ya watse.
“Yadda na ga wannan gagarumin taro wanda ya hada mutane wuri guda ba tare da nuna bambancin addini ba, lallai za a samu sauyin da ake bukata. Yana da matukar muhimmanci mu wanzar da gaskiya a tsakaninmu, saboda mu kasance jakadu na kwarai. Domin ta haka ne kadai za mu iya gudanar da abubuwa yadda ake bukata.
“Mun san cewa a wasu daga cikinmu sun fi wasu, amma mun kasance tare ne domin masu karfi su tallafa wa masu rauni ta yadda za a samu al’umma nagari.
Talaka na bukatar kiwon lafiya, abinci da sauran abubuwa masu yawa wanda idan har bai same su ba, to ba zai taba samun natsuwa ba. Mun dai samu mummunar tarihi ne na bullowar muyagun laifuka kamar irin sun kungiyoyi masu tayar da kayar baya da da ‘yan bindiga da dai sauran muyagun laifukan da mu taba ganin irinsu ba a cikin kasar nan sakamakon rashin tallafa wa al’umma.
“Dole ne mu fahimci abubuwan da suke faruwa domin mu cimma burikanmu na taimakon al’umma. Mun hadu ne a nan saboda mu yi aiki kafada da kafada cikin gaskiya da rikon amana domin kanmu. A bangaren wannan kungiya, za mu ci gaba da yin aiki domin tantance yankunan da suka fi bukatar taimako. Za mu tabbatar da cewa duk abin da muka tattara zai kai ga mutanen da ake bukata, domin za a dunga daukan bayanen abubuwan da muka yi ta yadda duniya za ta ga abun da muka yi.
Haka kuma ya ce duk da matsalolin al’umma suna da yawan gaske, amma za a fara bayar da tallafin ne ta bangaren kiwon lafiya, saboda yana yin muhallin da al’umma ke raywa a ciki.
Tun da farko, mataimakin sakataren kungiyar JAMAAT na kasa, Murtala Abdul-Rahman ya kawo tarihin kungiyar a takaice. Ya ce kungiya ce da take gudanar da ayyukanta a dukkan fadin duniya wanda take da rassa a kasarshe daban-daban da ke fadin duniya.
Ya ce jagoran Darikan Tijjaniyya, Sheik Ibrahim Inyass ne ya kirkiro kungiyar domin inganta rayuwar al’umma da ke rayuwa a ban kasa.
Mataimakin sakataren ya ce kungiyar tana kokarin habaka kowani fanni, amma tafi mayar da hankali ne wajen ilmantar da al’umma, sai kuma bangaren kiwon lafiya ta yadda take taimakawo ciki har da gina asibitoci da samar da kayayyakin aiki a bangaren kiwon lafiya da kuma bayar da tallafi ga bangaren.
A cewarsa, kungiyar tana kokarin kawar da talauci a cikin al’umma ta hanyar bayar da taimakon tallafin kudaden sana’a da samar da cibiyoyin koyon sana’o’i.
Ya ce kungiyar tana taimaka wa wadanda ibtila’i ya rutsa da su kamar na ambaliyar ruwa ko ‘yan gudun hijira, wanda take samar musu da abinci da kiwon lafiya da dai sauransu.
Mataimakin sakataren ya ce kungiyar tana tallafa wa mata wajen ganin sun dogara da kansu, wanda ya hada da tallafa musu wajen koyon sana’o’in hannu da kuma kare hakkinsu.
Ya ce kungiyar tana karfafa zumunci a tsakanin Musulmai da wadanda ba Musulmai ba domin samun fahimtar juna da zai kawo ci gaban al’umma, wanda take daukan nauyin shirya taron kara wa juna sani a tsakanin addinai a nan cikin gina Nijeriya da kuma kasashen ketare.
A cewarsa, kungiyar tana mayar da hankali kan habaka rayuwar matasa, wanda take samar da horo a tsakanin matasa domin inganta rayuwarsu. Ya ce kungiyar tana kai ziyara a gidagen yari domin tallafa wa dauraru, sannan tana shirya taron ciyarwa ga al’umma da kuma shirya gasa iri-iri a tsakanin matasa.
Da take mayar da jawabi a wurin taron hadin gwiwar, daya daga cikin ‘ya’yan kungiyar Rayuwa Da Zurfi, Iyabo Samuel ta bayyana cewa idan Allah ya yarda za a cimma abin ake bukata. Ta ce suna aiki ne kafada da kafada da sauran kungiyoyi da ke Dubai da Amurka wajen tallafa wa al’umma.
A cewarta, a kowani lokaci daga yanzu za su kawo na’urorir duba lafiyar mutane guda 37 da za a rarraba a dukkan jihohin Nijeriya ciki har da Abuja, sannan kuma kungiyar Rayuwa da Zurfi ne za ta ci gaba da kulawa da na’urorin.
Ta ce za su yi aiki kafada da kafada da kungiyar JAMAAT wajen taimakon al’umma, sannan suna bukatar hadin kai kowa da kowa domin inganta rayuwar al’ummar Nijeriya. Ta ce Allah ya albarkaci Nijeriya da arziki mai yawa, amma babu jagoranci mai kyau wanda hakan ne ya je fa al’ummar kasar cikin mawuyacin halai. Ta ce wannan ne ya sa suka mayar da hankali kan sake gina rayuwar mutane a Nijeriya.