Ahmed Umar" />

Jam’iyyun Adawa 31 Sun Yi Mubaya’a Ga Dan Takarar Gwamnan APC A Taraba

Kimanin jam’iyyun adawa 31 ne suka yi hadaka ta marama Dan Takaran Gwamna baya a karkashin tutar jam’iyar APC Alhaji Sani Abubakar Danladi don cancan tarsa na Kasan cewarsa adilin jagora kuma haziki acikin dukkannin ‘yan takara na jam’iyu da zasu shiga takara a 2019 jihar Taraba.
Abdullahi Bello wadda ke zama Shugaban Kungiyar hadakan yacyi nuni da cewa dukkanin shuwagabannin jam’iyun sun amince da raddaba hannu da yarda akan zacsu marama Dan Takaran jam’iyar APC baya a zaben 2019.
Bello yackara da cewa babu wani ko wata shugaba da aka tilasta don mika wuya ga wannan tafiyar kana yacyi nuni da cewa wannan yunkuri nasucne na ganin cewa jihar Taraba na fuskantar matsanancin hali da barazana ga jam’iyar PDP mai ci a jihar.
Ya ce wannan zabin sun yi nazari ne da kyutata ma al’umma da ya yi a kasancewarsa mukaddashin Gwamna na watanni shida kafin zaben 2015 da wasu aiyuka na hanyoyi da ya yi acikin jalingo fadar jihar da bunkasa rayuwar matasa na samar da aikinyi na dogaro dakai da tallafama a’luma.
“Muna sanardcaku cewa wannan zabi da mukayi yabiyo bayan tattanawa da mukayi tsakaninmu da sauran shugabannin jam’iyyu 31 da muka yi kuma muka cimma matsaya daya, shawari daya kana bakinmu guda dacewar Sani Danladi baya bambancin kabila ko bangaranci ko addini kuma shicne adilin jagora”.
Anasa jawabin dan takaran gwamnan APC Alhaji. Sani Abubakar Danladi ya ce yana mai farin ciki da wannan goyon baya da jam’iyu 31da suka yi ma sa, daga cikin dukkannin ‘yan takaran a jihar.

Exit mobile version